Karfin Hali: Dalibi Ya Cinye Ayabar N55m da Aka Ajiye a Gidan Tarihi, Yace Bai Karya Bane

Karfin Hali: Dalibi Ya Cinye Ayabar N55m da Aka Ajiye a Gidan Tarihi, Yace Bai Karya Bane

  • Wani matashi ya cizge ayaba mai darajar daloli tare da cinye ta a gidan tarihin da aka ajiye a kasar Korea ta Kudu a nahiyar Asia
  • Matashin ya cinye ayabar ne tare da bayyana cewa, yana jin yunwa kuma bai san dalilin da yasa za a ajiye ayabar ba a cinye ba
  • Wannan lamari ya ja hankalin jama’a da yawa a kafafen sada zumunta, inda ake ta cece-kuce kan yadda lamarin ya faru

Seoul, kasar Korea ta Kudu - Wani dalibi dan kasar Korea ta Kudu ya cinye wata ayaba da aka adana a matsayin kayan tarihi mai daraja na mai fikirar zane Maurizio Cattelan, inda ya ce yana jin yunwa saboda bai karya ba.

Aikin kawan mai suna ‘Comedian’ wani bangare ne na nuna aikin Cattalan da ke dauke da nunanniyar ayaba da ke sakale da igiyar roba a jikin bangon gidan tarihin Leeum da ke Seoul.

Kara karanta wannan

Kamar danki: Bidiyon wada lokacin da matarsa ke shafa masa ya jawo cece-kuce

Bayan cinye ayabar, dalibin mai suna Noh Huyn-Soo ya mayar da bawonta ya sakale a jikin bango kamar yadda ya samu.

Dalibin da ya cinye ayaba ya magantu
Dalibin da ya cinye ayaba a gidan tarihi | Hoto:nypost.com
Asali: UGC

Daga baya, gidan tarihin ya sake maye gurbin ayabar da wata ta daban, kamar yadda kafar labarai ta CNN ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka samu bidiyin cinye ayaba mai daraja

Abokin Noh ne ya dauki yadda lamarin da ya wakana a kasa da ‘yan mintuna, kamar dai yadda bidiyon aka ce ya yadu.

Gidan tarihin dai bai amsa sakon tambaya da BBC ta tura masa ba, amma ya sanar da manema labarai cewa, ba zai nemi dalibin ya biya ayabar ba.

Dama, ance ana sauya ayabar a duk bayan kwanaki biyu ko uku, wanda hakan ya nuna akwai sauki wajen maye gurbinta.

A tattaunawar matashin da manema labarai, bai nuna alamar dana-sani ba, kuma ya ce abin da ya yi kawai ya yi ne don jan hankali, don kuwa yana ta tambaryar dalilin sakale ayabar tun farko.

Kara karanta wannan

Karya kike: Bidiyon yadda yarinya ta fashe da kukan haushin ta ci maki 259 a JAMB

Ba wannan ne karon farko ba

Shi kansa mai aiki, Cattelan da aka sanar dashi ya ce babu komai, wanda ke nuna ba abu ne mai muhimmanci ba don ya cinye ayabar.

Hakazalika, ba wannan ne karon farko ba da ake cinye ayabar da aka ajiye a wurin a lokacin da masu ziyara suka kai ziyara gidan tarihin.

A shekarar 2019, wani mawaki, David Datuna ya taba cizge ayabar daga jikin katangar bayan da aka siyar da ita a kan $120,000 a Art Basel da Miami.

Wani dan Najerya kuwa, kifi ya kama mai launin gwal, kana ya nunawa duniya irin yadda kalarsa a kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel