Ku Taimake Ni: Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kifi Mai Launin Ruwan Gwal da Ya Kama, Bidiyon Ya Bazu

Ku Taimake Ni: Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kifi Mai Launin Ruwan Gwal da Ya Kama, Bidiyon Ya Bazu

  • Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan wani kifi mai launin ruwan gwal da ya kama
  • Mutumin ya baje kolin kifin sannan ya bukaci jama'a da su taimake shi wajen gano sunansa da kuma darajarsa don kada ya tafka kuskure
  • Wasu da suka yi ikirarin sanin kan kifaye sun fadi sunansa da kuma darajarsa, wasu kuma na ganin ba babban kamu ya yi ba

Wani bidiyo da ke nuna kifi mai launin ruwan gwal da wani dan Najeriya ya kama ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Mutumin ya wallafa bidiyon kifin a shafinsa na TikTok wanda har yanzu yana nan da ransa sannan ya bukaci masu kallo da su kawo masa dauki.

Matashi da kifi
Ku Taimake Ni: Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kifi Mai Launin Ruwan Gwal da Ya Kama, Bidiyon Ya Bazu Hoto: TikTok/@mr_unbreakable_kk
Asali: UGC

Ya bukaci mutane da su taimaka masa wajen gano sunan kifi saboda baya son cinye abun da ka iya kawo masa makudan kudade idan ya siyar da shi. Kalamansa:

Kara karanta wannan

Kamar Almara: Dan Wasan Da Ya Fi Kowa Kokari a Wasan Kwallo Ya Samu Kyautar Kwai

“Dan Allah ku tayani duba wannan kifin saboda ban taba ganin irin wannan launin ba. Ko dai kifin gwal ne...”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya tuna labarin wani mutumin Ughelli wanda ya kama kifin da zai iya sauya rayuwarsa amma ya cinye shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

User215561070743 ya ce:

“Ka zo arewa ya cika nan muna kiran shi kurongu mugun kifi. Hatta kifin na gasar soso.”

Pree me ta ce:

“Kifi ne da ba kasafai ake ganinsa ba, ana kiransa Corydoras melanotaenia ana yawan samunsa a Columbia. Na yi mamakin ganinsa naija.”

Nikky ta ce:

“Kifi yar kullun ce amma da kala daban, na sha gani da cin sa.”

rachesughdk ya ce:

“Kifi da muke ci a bayelsa ta koina ana ganin kifin a bayelsa yana da dadi fiye da mai fari da silba.”

Kara karanta wannan

Sai a kula: Kudaden bogi na kara yawa, mai POS ya ba da N1000 na bogi, an ki karba a kasuwa

Yaro dan shekara 16 da ke tuka adaidaita sahu ya samu tagomashi daga yan Najeriya

A wani labarin, wani yaro mai shekaru 16 ya samu tagomashin alkhairi daga yan Najeriya bayan wata matashiya ta wallafa labarinsa a shafinta.

Wasu bayin Allah ne suka hadawa yaron mai sana'ar tuka adaidaita sahu gudunmawar N82,000 domin ya koma makaranta kasancewar iyayensa talaakawa ne basu da karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel