Motoci Sun Ki Tafiya Bayan Da ’Yan Najeriya Suka Gama Shiga Za a Fitar Dasu Daga Sudan Zuwa Masar

Motoci Sun Ki Tafiya Bayan Da ’Yan Najeriya Suka Gama Shiga Za a Fitar Dasu Daga Sudan Zuwa Masar

  • ‘Yan Najeriya a Sudan sun bayyana yadda motoci suka ki tafiya bayan da aka gama loda komai saura tashi zuwa hanyar Masar
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya mazauna Sudan ke ta kokarin ganin sun fita daga kasar don gujewa yaki
  • A bangare guda, iyaye na ci gaba da ba da mafita ga ‘ya’yansu don tabbatar da sun fice daga kasar ba tare da wata matsala ba

Kasar Sudan - ‘Yan Najeriyan da suka makale a Sudan ake kokarin kwasowa sun shiga halin ni ‘ya su yayin da motocin da ke jigilarsu suka nuna musu wani hali.

A cewar majiya, bayan sun shirya, sun loda kayansu a motocin, sai direbobin suka ce babu inda za su tafi saboda wasu dalilai, Aminiya ta ruwaito.

Wani daga cikin daliban ya shaida cewa, tabbas sun shiga motoci a jiya Asabar domin dawo da su gida Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Buhari ya gano mafita, ya tura sojoji su kwaso masa 'yan Najeriya daga Sudan

Yadda 'yan Najeriya suka makale a Sudan
Motar da ya kwaso 'yan Najeriya daga Sudan | Hoto: platinumpost.ng
Asali: UGC

Halin da daliban ke ciki a halin yanzu

A cewar dalibin:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Amma kuma har za mu fara tafiya sai suka ce gwamnati ba ta biya su kudadensu ba; Shi ya sa suka ce ba za su tafi ba sai an biya su.
“Amma kayanmu suna cikin motar kuma su ma mototocin suna nan; an ce dai In sha Allahu yau (Lahadi) bayan asuba za mu tafi.”

Idan baku manta ba, bangarorin biyu da ke gwabza yaki a kasar ta Sudan sun ba da wa’adi, inda za su tsakaita wuta don barin ‘yan kasashen waje su samu damar fita daga kasar.

Sai dai, a yau Lahadi 30 Afirilu, 2023 ne wa’adin ya kare, har yanzu akwai sauran ‘yan Najeriyan da ke jiran a ceto su daga kasar.

Idan baku manta ba, gwamnatin Najeriya ta ce ta kashe dala miliyan 1.2 don tabbatar da kwaso 'yan kasarta da suka makale a Sudan, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kashe yaran da suka sace a Arewa, sun sako wasu 70

Iyaye na nemawa ‘ya’yansu mafita don barin Sudan

A bangare guda, iyaye a Najeriya na yin kokarin ganin yadda za su fitar da ‘ya’yansu daga kasar, inda suke shawartar yaransu da su koma Port Sudan don neman jirgi.

Tuni dai aka aka dakatar da zirga-zirgar jirage a birnin Khartoum na kasar, amma duk da haka ana ci gaba da ganin jiragen jifa-jifa.

A tsammanin iyaye, akwai yiwuwar samun jirgin da zai kwaso mutane daga Port Sudan zuwa Najeriya, dalilin ba da shawarin kenan.

A gefe guda, gwamnatin Najeriya ta tura jirgin sojin sama don kwaso ‘yan Najeriya daga Masar, wadanda aka ce sun isa can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel