'Yan Bindiga Sun Kashe Yara 2 da Suka Sace a Zamfara, Sun Sako 70 Cikin 85

'Yan Bindiga Sun Kashe Yara 2 da Suka Sace a Zamfara, Sun Sako 70 Cikin 85

  • ‘Yan bindigan da suka addabi jama’ar Zamfara sun yi aika-aika, sun harbe yara biyu da suka sace
  • Sun kuma sako 70 daga cikin sama da 85 da suka sace a jihar a makwanni uku da suka gabata
  • Ya zuwa yanzu, ana ta kokarin yiwa yaran jinya, sun samu matsala ta yunwa da bakar wahala daga tsagerun

Jihar Zamfara - ‘Yan bindiga sun sako mutum 70 cikin 85 da suka sace a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

An sace mutanen ne makwanni uku da suka gabata a gonakinus, inda aka ruwaito da yawansu mazauna yankin na Wanzamai ne da ke fama da rikicin ‘yan bindiga.

A cewar rahoto, an sace yara kanana ne a lokacin da suka je diban itace a daji, yayin da aka sace wasu manya kuwa a gonakinsu lokacin da suke sharar shirin damina.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hadarin mota ya kashe mutane 14 a jihar Arewa, an gagara gane su

An sako yara 70 cikin 85 da aka sace a Zamfara
Jihar Zamfara mai fama da tsagerun 'yan bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika, majiya ta bayyana cewa, akwai mata daga cikin wadanda wannan mummunan hari ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarjejeniyar da ta kai ga sako wadanda aka sacen

Wani mazaunin yankin, Sani Aliyu ya shaidawa jaridar cewa, an sako mutumm 70 cikin 85 din da aka sace ne a ranar Juma’a da dare.

A cewarsa:

“’Yan bindigan sun amince su sako yaran ne bayan da aka biya su Naira miliyan 6 a matsayin fansa. Da fari, sun ki sako wadanda suka sacen bayan an biya su Naira miliyan 3. Sun bukaci a basu sabbin babura guda biyu.”

An kashe wasu matasa biyu

Ya kara da cewa, an kuma harbe wasu matasan da suka yi kokarin guduwa daga hannun tsagerun ‘yan ta’addan, Eagle Online ta tattaro.

“’Yan ta’addan sun harbi matasa biyu da suka yi kokarin guduwa. Yaran da aka sako din sun rarrame kuma sun jikkata. Yanzu haka akwai sauran yara kusan 15 a hannunsu kuma bamu san dalilin rike su ba.

Kara karanta wannan

Namijin duniya: Lakcara mai mata hudu ya girgiza intanet, hotunansa da, matasa da 'ya'yan sun ba da sha'awa

“Wasu iyaye sun fashe da kuka lokacin da suka ga yanayin da yaransu ke ciki. Sun jejjeme saboda tsananin kunci da yunwa. Wadanda aka sako din yanzu haka suna karbar kulawar likitoci.”

Sai dai, duk da wadannan bayanai, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba, CSP Muhammad Shehu.

Baya ga rikicin 'yan bindiga, ana fama da yawaitar ayyukan ta'addanci da suka shafi kwacen waya a Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel