“Nagode Da Goyon Bayan Da Kuka Ba Gwamnatina”: Wike Ya Aike Sakon Barka Da Sallah Ga Musulmai

“Nagode Da Goyon Bayan Da Kuka Ba Gwamnatina”: Wike Ya Aike Sakon Barka Da Sallah Ga Musulmai

  • An ba Musulmai a jihar Ribas tabbacin samun muhalli mai kyau da wajen ibadah mai inganci
  • Gwamna Nyesom Wike ne ya bayar da tabbacin a yayin da yake aike sakon barka da sallah ga Musulmai
  • A sakonsa na fatan alkhairi, ya yi godiya ga Musulmai a jihar kan goyon bayan da suka baiwa gwamnatinsa

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya nuna godiyarsa ga Musulmai a jihar Ribas kan goyon bayan da suka ba gwamnatinsa.

Ya bayyana hakan ne a cikin sakon fatan alkhairi zuwa ga Musulmai a ranar Juma'a, 21 ga watan Afrilu yayin da suke bikin karamar sallah.

Gwamna Nyesome Wike na jihar Ribas
“Nagode Da Goyon Bayan Da Kuka Ba Gwamnatina”: Wike Ya Aike Sakon Barka Da Sallah Ga Musulmai Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, Wike ya jijinawa Musulmai kan kamalla azumin watan Ramadana cikin nasara da samun fa'idarsa.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

Gwamna Wike ya bukaci yan Najeriya da su nemi adalci, soyayya, gaskiya, daidaito da zaman lafiya da sauran jama'a a matsayin wasu darussa da suka koya a\ lokacin Ramadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa ya kamata a ci gaba da aiki da koyarwar Annabin tsira na hakuri, gaskiya da jajircewar da aka nuna tsawon lokacin Ramadana sannan a ci gaba da koyi da shi a rayuwa.

Sai dai kuma, gwamna Wike ya ba Musulmai tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yada juriya na addini da tabbatar da yanayin da ya dace da yancin bauta, jaridar Punch ta rahoto.

Buhari ya aika sakon sallah ga yan Najeriya

A wani labari makamancin wannan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta taka rawar gani sosai a zabukan da aka gudanar a fadin kasar nan, inda ya yi nuni da cewa an yi adalci a wanda ya sanya har wasu mambobin jam'iyyar sa ta APC, suka sha kaye a zaben.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Ta tabbata, Sarkin Musulmi ya ce gobe Juma'a ne karamar Sallah a Najeriya

Shugaban kasar ya bayyana cewa bai taba sanya bakinsa ba a harkar zaben saboda kada ya fifita wani ko wata.

Hakan na kunshe ne a cikin sakon barka da sallah da Buhari ya aikewa daukacin al'ummar Najeriya ta hannun bai ba shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu.

A yau Juma'a 21 ga watan Afrilu ne daukacin Musulman Najeriya suka gudanar da bikin karamar Sallah bayan kammala azumin Ramadana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel