Onoja, Adeyemi da Jamiu: Manyan ’Yan Siyasar APC 3 da Ke Son Maye Gurbin Yahay Bello Na Kogi

Onoja, Adeyemi da Jamiu: Manyan ’Yan Siyasar APC 3 da Ke Son Maye Gurbin Yahay Bello Na Kogi

Gabanin zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023, jam’iyyar APC ta tantance ‘yan takararta na gwamna.

Wani rahoton jaridar This Day ya nuna cewa, jam’iyyar ta tantance ‘yan takara 18 a babban birnin tarayya Abuja.

Daga cikin 18 da aka tantance, Legit.ng ta tattaro muku bayanan uku daga cikin wadanda suka yi fice a siyasar jihar Kogi.

'Yan siyasan da ke son maye gurbin Yahaya Bello
Onoja, Adeyemi, Jamiu da Yahaya | Hoto: Yahaya Bello, Edward Onoja, Smart Adeyemi, Jamiu Asuku Abdulkareem
Asali: Facebook

Hakazalika, hasashe ya nuna daya daga cikinsu na iya yin nasara a zaben fidda gwanin da a za a gudanar na jihar a watan Afrilu. Ga su kamar haka:

1. Edward Onoja

Daya daga cikin fitattun ‘yan takarar, Edward Onoja, shine mataimakin gwamnan jihar Kogi. Onoja dai na da alaka mai karfi tsakaninsa da uban gidansa, gwamna Yahaya Bello kuma yana da damar yin nasara a zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Onoja ya yi aiki a karkashin mulkin Yahaya Bello a matsayin shugaban ma’aikata tun farkon zaben gwamnan a 2016. A watan Oktoban 2019, ya zama mataimakin gwamnan jihar bayan tsoge Simon Achuba.

A ranar 16 ga watan Nuwamban 2019, an sake zabansa tare da Yahaya Bello, inda suka koma mulki a karo na biyu.

2. Sanata Smart Adeyemi

Sanata Smart Adeyemi a yanzu haka yana majalisar dattawa, inda yake wakiltar Kogi ta Yamma a majalisa ta taya. Kamar Onoja, Adeyemi na da alaka mai karfi da gwamna Yahaya Bello.

A 2019, gwamna Yahaya Bello ya yi amfani damarsa da ikonsa na siyasa don ganin Adeyemi ya zama sanata, inda ya nike abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye.

3. Jamiu AbdulKareem Asuku

Jamiu Abdulkareem Asuku ne shugaban ma’aikatan gwamnan APC a jihar Kogi, Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

Duk da cewa ba shi da tasiri mai karfi na siyasa kamar Onoja da sanata Adeyemi a jihar ta Kogi, amma zai iya yin nasarar samun goyon bayan Yahaya Bello.

Zaben 2023: INEC ta yi hayar lauyoyi don kare sakamakon zaben bana

A wani labarin, kunji yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi hayar manya kuma kwararrun lauyoyi domin kare sakamakon zaben 2023.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan siyasar kasar ke bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaben da aka yi bana.

INEC ta ce, tana da tabbacin gaskiya da bin ka’ida a zaben, don haka za ta kare kanta a gaban duk kotun da za a je.

Asali: Legit.ng

Online view pixel