Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta DSS Ta Yi Kira Ga Jama’a da Su Yi Taka-Tsan-Tsan, Akwai Matsala a Najeriya

Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta DSS Ta Yi Kira Ga Jama’a da Su Yi Taka-Tsan-Tsan, Akwai Matsala a Najeriya

  • Hukumar tsaro ta farin kaya ta gargadi abin da ka iya faruwa a Najeriya nan ba da jimawa ba na rashin tsaro
  • Wannan lamari na zuwa ne bayan da hukumar ta yi kira ga dagulewar zaman lafiya a lokacin zaben gwamna a Najeriya
  • Sanar da sakamakon zabe a jihar Zamfara ya zo da tsaiko, inda ‘yan daba suka lalata cibiyar yada fasaha ta NBTI

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana bankado wasu shirye-shirye daga wasu bata-gari da ke son kawo tsaiko da tashin hankali a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne makwanni biyu da hukumar ta yi gargadin aukuwar barkewar rikicin siyasa a kasar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hukumar ta yi kira ga shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a fannin da su bi doka da oda ko su tafi kotu idan basu gamsu da wani sashen zabe ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Yadda DSS suka gano shirin barna a Najeriya
Jami'an hukumar DSS a Najeriya | Hoto: blackboxnigeria.com
Asali: UGC

Abin da hukumar DSS ta hango

A cewar wata sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun kakakinta, Peter Afunanya, ta ce yayin da wasu ‘yan siyasa ke neman hakkinsu a kotu, wasu kuwa na tada hankali wajen tofa kalamai masu tada zaune tsaye.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta bayyana cewa, barkewar rashin tsaro da za a samu a Najeriya a wannan karon na da alaka da siyasa da kuma masu ruwa da tsaki a fannin.

Hakazalika, ta ba da shawarin al’umma su kwantar da hankali, inda tace ya kamata ‘yan siyasa su tafi daidai da tsarin dimokradiyya ba ta’addanci ba, rahoton Vanguard.

A daina yada labaran karya

A bangare guda, kakakin na DSS ya ce, ya kamata jama’a su kula da yadda ake yada labaran karya game da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Ya kuma shaida cewa, hukumar ba za ta juri yadda mutane ke tada hankali a kasar ba, za ta dauki matakin da suka dace.

Bayan kammala zaben gwamnoni a Najeriya, an samu barkewar rikici a yankuna daban-daban na kasar.

Yadda aka lalata cibiyar fasaha ta NBTI a Zamfara

Jim akdan bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Zamfara, wasu tsageru sun lalata cibiyar harkar fasaha ta NBTI da ke jihar.

A cewar majiya, an lalata kayayyakin da suka haura na N1bn, lamarin da ya jawo jimami ga manyan ma’aikatan cibiyar.

Ya zuwa yanzu, shugabannin cibiyar sun yi kira ga gwamnatoci da su kawo dauki don reage wa mutanen da lamarin ya shafa radadin rashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel