Yadda ’Yan Bangan Siyasa Suka Lalata Cibiyar Hada-Hadar Fasaha Ta NBTI a Jihar Zamfara

Yadda ’Yan Bangan Siyasa Suka Lalata Cibiyar Hada-Hadar Fasaha Ta NBTI a Jihar Zamfara

  • Wasu tsagerun ‘yan daba sun lalata cibiyar NBTI da ke jihar Zamfara a lokacin gangamin murnar lashe zaben Dauda Lawal
  • Wannan lamari ya kai asarar makudan kudaden da aka zuba jari a ciki, kamar yadda wani babban jami’i ya tabbatar
  • Rikici ya barke a wasu yankunan kasar nan bayan kammala zaben gwamna, ciki har da jihar Kano da ke a yankin da Zamfara take

Jihar Zamfara - Wasu da ake daba ne sun tafka barna a ginin cibiyar hada-hadar fasaha ta National Board for Technology Incubation (NBTI) da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya.

Kamfanin dillacin labarai na NAN ya ruwaito cewa, ‘yan daban sun yi amfani da gangamin murnar lashe zaben dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP ne wajen aikata wannan barnar.

Muhammadu Jazuli, wani mamban NBTI a Arewa maso Yamma ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Gusau bayan duba ga irin barnar da aka tafka, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: DSS Ta Damƙe Ɗan Majalisa Kan Hannu a Laifin da Ya Shafi Karancin Naira

Yadda 'yan daba suka yi barna a Zamfara
Jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Irin asarar da aka tafka ta biliyoyi

A cewarsa, an lalata kayayyakin gwamnati da kadarori masu darajar da suka kai akalla N1bn a lokacin da ‘yan daban suka mamaye ofishin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Kun san gwamnatin tarayya ce ta kafa cibiyar a 1999 kuma dukkan abin da gwamnati ta zuba a cibiyar a cikin shekaru 23 kusan Naira biliyan 1 ‘yan daba sun lalata.
“Wannan lamari ne mara dadi, wannan mumman abu ne saboda ba kayan gwamnati ne kadai aka taba ba, har da kayan 'yan kasuwa da gama-garin jama’a da suka zuba hannun jarinsu.
“Da yawan ‘yan kasuwa ko masu zuba hannun jari sun ci bashi ne daga banki don sayen kayayyakin, har kofofi da tagogin wannan ofis din sai da aka cire, dukkan kujeru, komai an sace.
"Kamar yadda kuke gani bamu da sauran kujera ko daya a wannan cibiyar, ba zan iya jure wannan haukan ba.”

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Hana Fita Daga Wayewar Gari Zuwa Dare

Ya kamata gwamnati ta kawo dauki

A cewar Jazuli, barnar da aka yi abin damuwa ce duba da muhimmancin wannan cibiya a jihar ta Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su binciki lamarin tare da tabbatar da an kama tare da hukunta wadanda suka kitsa wannan mummunan aikin.

Jazuli ya kuma bukaci gwamnatin jihar da ta tarayya da su kawo dauki ga cibiyar don ci gaba da aikinta kamar yadda ta saba.

A irin tashin hankalin nan ne aka kone gidan mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara a jihar Kano bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel