Abinda Ya Sa Bola Tinubu Ya Fita Najeriya Zuwa Kasar Waje, Tunde

Abinda Ya Sa Bola Tinubu Ya Fita Najeriya Zuwa Kasar Waje, Tunde

  • Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya tafi kasar waje domin ya samu hutu bayan gama kamfe da babban zaben 2023
  • Mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Legas ɗin, Tunde Rahman, ya gargadi kafafen watsa labarai su guji yaɗa labaran karya
  • Ya ce Tinubu zai ɗan huta a Faransa da Landan, daga nan zai wuce Ƙasa mai tsarki ya yi Umrah

Abuja - Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tafi ƙasar waje ne domin ya huta kuma ya fara shirin karban mulki gabanin ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Legas ɗin, Tunde Rahman, ne ya bayyana haka yayin da ake yaɗa jita-jita kan tafiyar Tinubu.

Bola Ahmed Tinubu.
Abinda Ya Sa Bola Tinubu Ya Fita Najeriya Zuwa Kasar Waje, Tunde Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya ce Mista Rahman ya roki kafafen watsa labarai su daina wallafa labaran da ba su tabbata ba game da uban gidansa.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Bola Tinubu ya fita Najeriya zuwa waje ne domin a duba lafiyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene gaskiyar abinda ya tafi yi a waje?

A wata sanarwa da Tunde Rahman ya fitar ranar Laraba, ya ce Tinubu ya yanke shawarin ɗaukar hutu bayan kammala harkokin kamfe da babban zaɓe.

Ya ce:

"Bayan yawace-yawace lokacin kakar yakin neman zabe da kuma babban zaɓen 2023 shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi tafiya zuwa ƙasar waje."
"Ya fita ne domin samun hutu kuma ya shirya wa bikin karɓan mulki gabanin zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Ya bar filin jirgin Murtala Muhammed da ke Ikeja zuwa Turai ranar Talata da daddare."
"Zababben shugaban ya tafi hutu ƙasar Faransa da Landan bayan gama kamfe da zaɓe. Zai wuce Saudiyya ya gudanar da aikin Umrah da Azumin Ramadan da za'a fara ranar Alhamis."

Kara karanta wannan

Canjin kudi, Kanu, ASUU da Abubuwa 5 da Tinubu Zai Ci Karo da Su da Ya Shiga Aso Rock

Ya kara da bayanin cewa a wannan lokacin da zai shafe a waje, Tinubu zai tsara duk wani shirin karban mulki daga hannun shugaba mai barin gado, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

INEC ta bayyana sakamakon zaben Abiya

A wani labarin kuma Hukumar zabe ta ƙasa ta ayyana ɗan takarar Labour Party a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Abiya

Hakan na nufin LP ta kawo karshen shekara 24 da jam'iyyar PDP ta kwashe tana mulkin jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel