PDP Ta Lashe Karamar Hukumar Karshe da INEC Ta Sanar a Jihar Abiya

PDP Ta Lashe Karamar Hukumar Karshe da INEC Ta Sanar a Jihar Abiya

  • Labour Party ta kawo karshen mulkin jam'iyyar PDP na tsawon shekaru 24 a jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya
  • INEC ta ayyana dan takrar gwamna a inuwar LP, Alex Otti, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala ranar Asabar
  • An kai ruwa rana yayin tattara sakamakon zaɓen wanda sai yau aka sanar da sakamakon karamar hukumar ƙarshe

Abia - Daga ƙarshe hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sakamakom zaben gwamna daga ƙaramar hukumar Obingwa ta ƙarshe a jihar Abiya.

Daily Trust ta rahoto cewa INEC ta sanar da sakamakon Obingwa, karamar hukumar da ta haddasa ruɗani da kace-nace a cibiyar tattara sakamako da ke Umuahia, babban birnin jihar Abiya.

Alex Otti.
Zababben gwamnan jihar Abiya, Alex Otti Hoto: Alex Otti
Asali: Twitter

Sakamakon ya nuna ɗan takarar gwamna a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Okey Ahaiwe, ya lallasa babban abokin karawarsa na Labour Party, Alex Otti, da ƙuri'a mafi rinjaye.

Kara karanta wannan

Bayan Kwanaki Uku, INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben 'Yan Majalisar Dokokin Jihar da PDP Ke Mulki

Cikakken sakamakon zaben gwamna daga Obingwa LG

ADC 37

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ADP 19

APC 721

APGA 1445

APM 18

APP 383

BP 113

LP 3776

NNPP 41

NRM 48

PDP 9962

PRP 12

SDP 55

YPP 3101

ZLP 48

INEC ta faɗi wanda ya lashe zaben gwamnan Abiya

Bayan karban wannan sakamakon, INEC ta ayyana dan takarar Labour Party, Alex Otti, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Abiya.

Mista Otti, tsohon Darakta a Diamond Bank Plc, ya samu kuri'u 175,467, ya lallasa takwaransa na PDP kuma tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Okey Ahaiwe, wanda ya samu kuri'u 88,529.

Baturen zaben jihar shugaban jami'ar fasaha ta tarayya da ke, Owerri, jihar Imo (FUTO), Farfesa Nnenna Otti, ne ya sanar da wanda ya samu nasara bayan gama tattara sakamako.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Zanga-Zanga Ke Gudana a Ofishin INEC Kan Ayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Wata Jiha

Tribune ta ce an samu tsaiko a tattara sakamkon zaben gwamnan Abuya har ta kai ga dakatarwa bayan rigingimun da suka biyo baya kan zargin maguɗi.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Abinda Gwamnonin PDP 5 Suka Ƙulla a Zaben Tinubu

Gwamnan jihar Ribas ya ce babu lokacin da gwamnonin G5 suka zauna suka yamke goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Maimakon haƙa Wike ya bayyana abu ɗaya da suka cimma wa game da zaven shugaban kasan da aka kammala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel