Wani Atiku Ya Caccaki Gwamna Wike Saboda ‘Yaudarar’ Gwamnonin G5 Na Jam’iyyar

Wani Atiku Ya Caccaki Gwamna Wike Saboda ‘Yaudarar’ Gwamnonin G5 Na Jam’iyyar

  • Wani hadimin Atiku ya yiwa gwamna Wike wankin babban bargo bayan da yace ya ji dadin sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi
  • Wannan na zuwa ne bayan da Wike yace shi yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Labour ne, Peter Obi
  • An yi zaben sanataoci, kusan dukkan gwamnonin G5 da ke adawa da Atiku sun fadi a zaben da aka gudanar a watan jiya

Najeriya - Hadimin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya zargi gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da yaudarar gwamnonin PDP na G5.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mr. Phrank Shaibu ya ce, babatun Wike bai da nasaba da tabbatar da Kudancin Najeriya ne ya samar da shugaban kasa.

Ya siffanta Wike da wanda ya yaudari gwamnonin G5 masu adawa da Atiku don kawai ya cimma manufarsa ta siyasa, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bwacha: Kwanaki Kadan Suka Rage a Zabi Gwamna, APC Ta Dakatar da ‘Dan Takaranta

Hadimin Atiku ya caccaki Wike
Dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yadda hadimin Atiku ya caccaki Wike

A cewar sanarwar da Shaibu ya fitar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Kiyayyar Wike ga Atiku Abubakar ba ta da alaka da tsarin shiyya-shiyya. Kawai yana babatu ne saboda ya fadi a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na PDP. Bayan shan kaye, ya yaudari gwamnoni hudu da su shiga sahun gangaminsa mara ma’ana.
“Gwamnonin G5 guda uku sun yi mummunan faduwa a zaben sanata, ciki har da gwamna Okezie Ikpeazu, wanda, a matsayinsa na gwamna mai ci ya zo na uku a mazabar sanata ta Abia Sourth.”

Makomar Makinde na cikin rikici

Hakazalika, ya bayyana yadda makomar gwamna Seyi Makinde ka iya kasancewa saboda yadda ya barar da kujerun sanatan PDP uku a zaben da ya gabata, Info Daily ta tattaro.

Ya kuma kara da cewa:

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zaben Gwamna: APC Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al'ummar Wata Jihar Kudu

“Wike bai zauna da mambobin G5 ko sau daya ba, inda ya yi watsi dasu tunda suka sha kaye. Yana ta murna da sakamakon zabe, duk da cewa mutanensa duk sun fadi. Wannan shine irin halinsa, amma a haka, yake cewa bai ci dunduniyar jam’iyya ba.”

Obi ne gwarzon zaben bana

A wani labarin, kun ji yadda gwamna Wike ya bayyana jin dadinsa ga sakamakon zaben bana na shugaban kasa.

Ya ce, ko ba komai, Peter Obi ya haramtawa ‘yan Arewa ci gaba da jan ragamar kasan bayan shugaban Buhari.

A baya ya bayyana adawarsa da yadda jam’iyyarsu ta PDP ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel