Jiragen Rundunar Soji Guda Biyu Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Sama

Jiragen Rundunar Soji Guda Biyu Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Sama

  • Jiragen sama 2 mallakin rundunar sojin saman ƙasar Italiya sun yi karo a sararin sama yayin da suke shawagin atisaye
  • Firaministan ƙasar, Giorgia Meloni, ta ce hatsarin wanda ya auku ranar Talata 7 ga watan Maris, ya yi ajalin matukan jirgin 2
  • Har kawo yanzun ba'a bayyana musabbabin abinda ya haddasa haɗarin ba, Sojoji sun ce ya faru ana cikin ɗaukar horo

Jiragen rundunar sojin sama ta ƙasar Italiya guda biyu sun yi karo da juna a sararin samaniya yayin shawagin ɗaukar horo ranar Talata 7 ga watan Maris, 2023.

Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, Firaministan kasar Italiya, Giorgia Meloni, ta ce hatsarin wanda ya auku a arewa maso yammacin Rome, ya yi ajalin matuƙan da ke cikin jiragen.

Hatsarin jiragen sojoji.
Wani sashin jirgin da ya yi haɗari a Italiya Hoto: channelstv
Asali: UGC

A wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar, ta ce matuƙa biyu ne a cikin jirgin ɗaukar horo mai lamba U-208 kuma suna cikin shawagin ƙara ilimi ne lamarin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

Channels tv ta ruwaito cewa har kawo yanzun mahukunta a ƙasar ba su gano asalin abinda ya haddasa karon jiragen ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Firaminista ta aike da sakon ta'aziyya

"Mun kaɗu lokacin da muka ji labarin mutuwar matuƙan jirgi guda biyu na rundunar Sojin sama sa'ilin da suke atisayen ɗaukar horo a kusa da Guidonia,” inji Meloni.

Daga nan sai Firaministan ta miƙa sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan matuƙan jirgin da kuma ɗaukacin mambobin rundunar sojin saman ƙasar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Jirgin sama kirar U-208 mai matsakaicin nauyi ne kuma yana da inji guda ɗaya, sannan yana iya ɗaukar fasinjoji huɗu da kuma matuƙinsa guda ɗaya.

Bugu da ƙari, an ce irin wannan jirgin saman na da ƙarfin gudu a sararin sama da ya kai kilo mita 285km (177 mph).

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

Jirgin Sama Dauke da Fasinjojin Ya Bace Bat a Sararin Samaniya

A wani labarin kuma kun ji cewa Jirgin sama da ya ɗauko Jamusawa ya ɓace bat a samaniya bayan ya taso daga ƙasar Mexico

Bayanai sun nuna cewa sadarwa da Jirgin ta datse ne yayin da ya nufi gabashin ƙasar Costa Rica da tsakar dare.

Ministan tsaro a ƙasar Costa Rica ya tabbatar da cewa tuni suka ɗauki matakan da ya dace domin zakulo inda jirgin ya shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel