Dole a Yi Wani Abu Kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Kotun Koli Ya Koka

Dole a Yi Wani Abu Kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Kotun Koli Ya Koka

  • Kotun koli a Najeriya ya koka kan yadda ake yawan kawo kararraki marasa ma’ana a gabansa babu gaira babu dalili mai mai karfi
  • Wannan na fitowa ne daga bakin alkalan da suka zauna don yin shari’a a karar da gwamnoni suka shigar kan gwamnatin tarayya
  • Daya daga cikin alkalan ta bayyana dalilin da yasa ake kai batutuwa gaban kotu koli, kotun na neman a yi gyara a kundin tsarin mulkin kasar

FCT, Abuja - Kotun koli a Najeriya ya koka kan tarin aikin da ke gabansa, wanda ya daura alhakinsa ga gibi a kundin tsarin mulkin kasar, Daily Trust.

A zamansa na ranar Laraba 22 Faburairu, 2023 kan karar gwamnoni da gwamnatin tarayya kan dokar kudi, kotun ya ce an tara masa ayyuka da yawa ba bai kamata a kawo su gabansa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An dage ci gaba da zama a karar gwamnoni da FG kan dokar Naira

Wannan batu na fitowa ne daga ba kin alkalin da ya jagoranci gamayyar alkalai bakwai na kotun, mai shari’a Inyang Okoro.

Kotun koli ya nemi a gyara kundin tsarin mulkin Najeriya
Zaman da alkalai ke yi a kotun kolin Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Laifin majalisar dokoki ne, inji kotun koli

Ya bayyana cewa, majalisar dokokin kasar bata mai da hankali ga bangarori masu muhimmanci a lokacin kwaskwarima, illa dai ga abubuwan da suka shafe ta, The Nigerian Lawyer ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, cewa ya yi:

“Mata ta mari mijinta, sai su kotun koli, saboda meye, abin da mai gida zai iya shawo kansa cikin sauki amma an kawo kotun koli?
“Mai gida da dan haya sun yi musu, an kawo batu kotun koli.
“Wadanda ke da damar gyara kudin tsarin mulkin kasarmu ya kamata su yi wani abu.”

A nata bangare, mai shari’a Amina Augie ta ce, gaggawar da ake na kawo komai gaban kotun koli ba komai bane illa kawai hankoron lauyoyi su girma, su zama SAN.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Ana dab da zabe, kotu ta kori dan takarar gwamnan PDP a wata jiha

Yadda ta kaya a zaman kotun koli a karar su El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji yadda kotun kolin ta yi hukuncin dage ci gaba da zaman shari’a tsakanin gwamnonin Najeriya sama da 10 da gwamnatin tarayya kan batun da ya shafi wa’adin daiana amfani da tsoffin kudi.

Kotun ta dage ci gaba da zaman shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Maris mai zuwa, don daddale komai na abin da gwamnonin suka gabatar.

‘Yan Najeriya na ci gaba da zaman kunci da wahalar sabbin Naira tun bayan karewar wa’adin farko da Babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel