'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna)

'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna)

Daya daga cikin babban abu a duniyar nan mai girgiza zukatan jama'a shine mutuwa, duk da kuwa an san dole ne kowa ya dandanata.

Babu shakka mutuwa dole ce, tunda Allah ne ya tabbatar da cewa kowacce rai sai ta dandana zafinta.

Masana'antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, ta dandana rashe-rashe da dama. Daga ciki kuwa akwai na 'yan matan masana'antar wadanda suka shahara.

Ga wasu daga cikin 'yan matan masana'antar da suka rasa rayukansu da kananan shekarunsu:

1. Fadila Muhammad: Fitacciyar jarumar masana'antar fina-finan hausa wacce ta yi sharafi daga shekarar 2011 zuwa 2014, ta rasu a ranar 29 ga watan Augustan 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Tana daya daga cikin jarumai masu matukar salo da farin jini a masana'antar.

Matashiyar jarumar tana da wani irin salo na bayyana a wasan kwaikwayo, wanda ke saka zukatan masu kallo cikin nishadi.

Tauraruwarta ta fara haskawa tun bayan da ta fito a fina-finai masu suna Hubbi da Basaja. Babu shakka wadannan fina-finan sun saka sunanta ya dauku ga ma'abota kallon fina-finan Hausa.

Babu shakka za a ci gaba da tunawa da ita matukar za a ambaci tarihin masana'antar fina-finan. Ta rasu tana da shekaru 27 a duniya.

'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna)
'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna). Hoto daga BBC
Asali: Instagram

2. Maryam Aliyu: Marigayiya Maryam na daga cikin 'yan matan masana'antar fina-finan hausa masu matukar farin jini a lokacin da take raye.

Ta bayyana a fitattun fina-finai masu suna Sarki Goma, Rugunstumi da Attajirai. Ta rasu ne yayin da take nakuda za ta haihu a cikin watan Afirilun 2011.

Ta rasu tana da shekaru 25 a duniya, kuma ta bar mijinta Musbahu M. Ahmed, wanda jarumi a masana'antar.

'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna)
'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna). Hoto daga Kannywoodnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fitacciyar jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta sanar da daina fitowa a fim

3. Safiyya Ahmed: Marigayiyar jaruma Safiyya ta rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiyar da tayi a garin Kano a 2010. Hazikar jarumar na cikin sharafinta yayin da mutuwa ta dauketa.

Babu shakka za a ci gaba da tunawa da ita a kan gudumawar da ta bada wajen ficen masana'antar. Wasu daga cikin fitattun fina-finan jarumar sun hada da Ruduntsumi da Gobe ma Rana ce. Ta rasu tana da shekaru 27.

'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna)
'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna). Hoto daga Kannywoodnews
Asali: Twitter

4. Balaraba Muhammad: Balaraba jaruma ce da ta yi farin jini a masana'antar fina-finai sakamakon hazaka da iya gogewa a wasan kwaikwayo da tayi.

Allah ya karba rayuwar jaruma Balaraba Muhammad a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2002.

Ta rasu sakamakon mummunan hatsarin da suka yi a kan titin Zaria zuwa Kano.

Marigayiyar ta rasu yayin da ake kan hanyar kai ta dakin mijinta bayan daura musu aure da aka yi da jarumi Shu'aibu Lawan, wanda aka fi sani da Kumurci.

Za a ci gaba da tunawa da jarumar mai shekaru 18, sakamakon rawar da ta taka a fina-finan Furuci, Dawayye da Tasiri.

'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna)
'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu (Hotuna). Hoto daga kannywood news
Asali: Facebook

Allah ya jikansu da gafara, ya kyautata zuwan tamu. Ameen

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng