Kwankwaso Ya Lallasa Tinubu a Karamar Hukumar Gwamnan Ganduje Na Kano

Kwankwaso Ya Lallasa Tinubu a Karamar Hukumar Gwamnan Ganduje Na Kano

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya smau naaara kan Bola Tinubu a karamar hukumar gwamna Ganduje a jihar Kano
  • Gwamnan ya fito nr daga kauyen Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa amma bai iya kawowa Tinubu yankinba
  • INEC na ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa daga kananan hukumon jihar Kano

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya sha kaye a ƙaramar hukumarsa hamnun ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Daily trust ta tattaro cewa gwamnan Kano mai ci ɗan asalin ƙauyen Ganduje ne da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Gwamna Abdullahi Ganduje.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Ganduje

Baturen zaɓe na Dawakin Tofa, Adamu Jibril, ya bayyana sakamakon zabe da cewa jam'iyyar Ganduje watau APC ta samu kuri'u 16,773 yayin da NNPP mai daɗi ta samu kuri'u 25,072.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Peter ya lashe zabe a wata karamar hukumar jihar Arewa

Alhaji Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 2,477 yayin da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya tashi da kuri'u 202.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Ganduje na ɗaya daga cikin masu yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, na sahun gaba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC na ci gaba da aikin tattara sakamakon zaben da aka kammala daga kananan hukumomin Kano.

Kawo yanzu dai ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai kayan marmari ne ya ke gaba bayan sanar da sakamakon kananan hukumomi sama da 10 ciƙin 44 da Kano ta ƙunsa.

Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ne ke take masa baya yayin da tsohom mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na uku.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Guguwa: Jam'iyyar Labour Ta Kawo Karshen Mulkin Dan Majalisa Bayan Zango Hudu A Kaduna

A ranar Asabae 25 ga watan Fabrairu, 2023, yan Najeriya mafi yawan ssassan kasa suka kaɗa kuri'unsu don zaben wanda zai gaji shugaban ƙaaa, Muhammadu Buhari.

Atiku Ya Samu Nasara a Kananan Hukumomi 18 Na Jihar Osun

A wani labarin kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ta lallasa Tinubu, ya lasje zaɓe a kananan hukumomi 18 a jihar Osun kawo yanzu.

Bola Tinubu, wanda ake hasashen zai share kuri'un jihar ga sha mamaki ganin yadda mutane suka kaurace masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel