'Yan Daba Sun Kona Akwatuna da Kayan Aikin Zabe a Benin

'Yan Daba Sun Kona Akwatuna da Kayan Aikin Zabe a Benin

  • Wani rahoto mara dadi da ke iso mu ya bayyana cewa, wasu 'yan daba sun kone akwatunan zabe a jihar Edo
  • Wannan lamarin ya faru ne bayan da masu kada kuri'u suka gama yin zabe kafin a fara kirgan abin da aka tara a akwatunan
  • An samu tashin hankali a wuraren kada kuri'u a wasu bangarori daban-daban na Najeriya daga 'yan daban siyasa

Benin, jihar Edo - Masu kada kuri'u sun yi gudun fanfalaki yayin da wasu 'yan daba suka kai farmaki kan rumfar zabe ta Uwelu a birnin Benin na jihar Edo, sun kone akwatuna bayan an gama kada kuri'u.

Yayin da ake ci gaba da kada kuri'u, a bayyane yake cewa, jama'ar yankin sun kada wa jam'iyyar Labour kuri'unsu, rahoton Punch.

Don tabbatar da kawo tsaiko, 'yan daban sun zo cikin makarantar da ake zaben, lamarin da ya kora masu kada kuri'u don gudu kada a cutar dasu.

Kara karanta wannan

Ba a gama zabe ba: Bidiyo ya nuna yadda ake kada kuri'a cikin dare a wata jihar Bauchi

'Yan daba sun yi barna a Benin
Yadda aka yi barna a rumfar zaben Benin | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daya daga cikin masu kada kuri'un da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda yace mutane da yawa ne suka zabi Peter Obi a rumfar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Kowa Peter Obi ya zaba a wannan rumfar kuma yana kan ganiyar nasara kafin 'yan daban su zo su hargitsa zaben. Idan za a bamu damar sake yin zabe, LP din dai za mu zaba."

A wannan shekarar ma bata sauya zane ba, domin an samu lokuta da yawa da 'yan daba suka farmaki rumfunan zabe daban-daban a jihohin Najeriya a zaben bana.

'Yan daba sun farmaki jami'an hukumar EFCC a jihar Imo da kuma Abuja

A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka kai farmaki kan jami'an hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Jami'an sun fito aikin tabbatar da ba a yi siye da siyar da kuri'u ba a filayen da aka yi zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Najeriya.

Wannan lamarin ya zo da tsaiko, domin an yi kaca-kaca da wata motar da jami'an ke tafiya a cikinta a cikin birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel