Wasu ’Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Jami’an Hukumar EFCC a Abuja da Jihar Imo

Wasu ’Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Jami’an Hukumar EFCC a Abuja da Jihar Imo

  • Wasu tsagerun ‘yan daba sun farmaki motar jami’an hukumar EFCC a lokacin da suke aikin sa ido kan zaben bana
  • Wannan lamari ya faru ne a Abuja da kuma jihar Imo, inda aka kama wani mai siyan kuri’u a babban birnin tarayya
  • A wannan shekarar ma an samu tashin-tashina a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a Najeriya

FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayyana cewa, wasu tsagerun ‘yan daba sun farmaki jami’anta d ake aikin sintirin sa ido kan zaben ranar Asabar.

Hukumar ta bayyana wannan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu a Abuja, inda tace an farmaki jami’an nata ne a Abuja da kuma jihar Imo.

A cewar sanarwar da kakakinta, Wilsom Uwujaren ya fitar, an farmake su ne a fadar sarkin Bwari da ke Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sace na'urar aikin zabe a jihar su Buhari da kuma wata jihar

Yadda aka farmaki jami'an EFCC a Imo da Abuja
Barnar da aka yiwa jami'an EFCC a Abuja da Imo | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Yadda aka farmaki hukumar EFCC

EFCC ta ce an farmake ta ne bayan da jami’anta suka kama wasu da ake zargin ya kitsa siyan kuri’u a rumfar zaben da Science Primary School da ke Bwari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

“Tawagar ta kame wani da ake zargi, mai kimanin shekaru 30, kuma an kwato daga hannunsa jerin sunayen wadanda za a ba kudi ta hanyar amfani da manhajar tura kudi ta banki.”

Hukumar ta ce, yayin da jami’an ke kokarin tafiya da mutumin ne daga rumfar wasu ‘yan daba suka farmaki su tare da fashe gilasan motar.

Yadda jami’an suka tsira daga ‘yan daba

Sanarwar ta kuma kara da cewa, ‘yan daban sun tsere ne kawai lokacin da jami’an suka yi harbin tsoratarwa da bindiga, TheCable ta ruwaito.

Wasu mambobin tagawar jami’an tsaron hadin gwiwa na JTF ne suka kuma taimakawa jami’an hukumar a wannan kazamin yanayi.

Kara karanta wannan

Jajiberin zabe: Tashin hankali yayin da aka dasa bam a gidan dan takarar majalisa na APC

An yi hargitsi a zaben bana

Bata sauya zane ba, a wannan karon ma an samu tashin-tashina a wuraren da aka kada kuri’u a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a Najeriya.

A baya kun ji yadda jami’an hukumar EFCC suka kame daraktan kamfen gwamnan jihar Benue dauke da kudade a hanyar zuwa rumfar zabe.

Wannan lamari ya tayar wa gwamnan hankali, ya bayyana rashin jin dadinsa tare da yin martani mai daukar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel