'Yan Ta’adda Sun Dasa Bam a Gidan Dan Takarar Majalisar Dokoki a Jihar Ribas

'Yan Ta’adda Sun Dasa Bam a Gidan Dan Takarar Majalisar Dokoki a Jihar Ribas

  • Rahotannin da muke samu daga jihar Ribas na bayyana cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun farmaki gidan dan takarar APC
  • Wannan lamari ya faru ne kwanaki biyu bayan da aka farmake shi a wurin taron kamfen da ya yi a mazabarsa
  • Ana ci gaba da samun munanan hare-hare tun bayan da ya saura kwanaki kadan a yi zaben shugaban kasa a Najeriya

Jihar Ribas - Dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Ribas a mazabar Etche, Hon. Charles Anyanwu ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan harin da aka kai gidansa da ke Fatakwal.

Rahoton da muke samu daga jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, wasu ‘yan ta’adda ne suka kai mummunan farmaki tare da dasa bam a gidan dan siyasan.

A kwanakin baya, dan siyasan ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wa tawagar motocinsa wuta a lokacin da ya fito kamfen a Etche.

Kara karanta wannan

Rikicin zabe: An farmaki tawagar matar dan takarar majalisan PDP a Zamfara, an harbi 'yan sanda

An farmaki gidan dan takarar APC a jihar Ribas
Barnar da aka yi a gidan dan takarar | Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Majiyoyin kusa da dan takarar sun tabbatarwa jaridar cewa, ‘yan ta’addan sun farmaki gidan Anyanwu ne tare da dasa bam da sauran kayayyakin tashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin an samu asarar rai a harin?

An ce ba a samu asarar rau a harin ba, amma dan an lalata kadarori masu daraja a cikin gidan nasa, Within Nigeria ta tattaro.

Kakakin rudunar ‘yan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko ya ce ana ci gaba da bincike kan mummunan lamarin.

Yayin da zabe ya karato, ana ci gaba da kai munanan hare-hare kan ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban a kasar nan.

A cikin makon nan ne Kwankwaso ya yi kamfen a jihar Kano, inda aka samu wasu tsagerun da suka farmaki magoya bayansa tare da kone motoci da lalata dukiyar al’umma a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan halartar taro kan zaben gobe, shugabar karamar hukuma ta kwanta dama

Rundunar soji za ta dauki mataki kan masu kawo tsaiko ga zaben bana

A wani labarin kuma, kun ji yadda rundunar sojin Najeriya ta bayyana matsayarta game da shirin zaben 2023 da ke tafe a gobe Asabar 25 ga watan Faburairu.

Rundunar ta yi gargadin cewa, za ta dauki mataki kan dukkan wadanda ke kokarin kawo tsaiko ga zaben na bana.

A cewar hukumar, za ta yi amfani da karfin soja wajen tangwara duk wani mai shirin yiwa zaben gan-gani bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel