Ortom Ya Fusata Yayin da EFCC Ta Kama Daraktan Yakin Neman Zabensa da Tsabar Kudi N100k

Ortom Ya Fusata Yayin da EFCC Ta Kama Daraktan Yakin Neman Zabensa da Tsabar Kudi N100k

  • Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda EFCC ta kama daraktan kamfen dinsa a jiharsa
  • Gwamna Ortom ya kuma ji dadin yadda al’ummar jiharsa suka fito domin kada kuri’unsu a zaben bana da aka yi
  • Halazalika, ya yabawa INEC bisa tsara zabe cikin tsanaki kuma na gaskiya babu muna-muna a ciki ko kadan

Jihar Benue - Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta EFCC ta kame daraktan kamfen gwamnan PDP Samuel Ortom na jihar Benue dauke da kudade N100,000 a ranar zabe.

The Nation ta ruwaito cewa, an kama Dr. Cletus Tyokaa ne a kan hanyarsa ta zuwa garinsu, Daudu a karamar hukuma Guma ta jihar.

Idan baku manta ba, hukumar EFCC ta ce za ta sanya ido kan masu siyan kuri’u a zabukan da za a yi shekarar nan.

Kara karanta wannan

Fata na 1:El-Rufai ya yiwa Tinubu addu'a, ya fadi matsalar da aka samu a jiharsa a wurin zabe

An kama daraktan kamfen Samuel Ortom da kudi
Samuel Ortom, gwamnan jihar Banue | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamna Ortom ya fusata, ya yi martani

Gwamna Ortom, a lokacin da yake martani ga lamarin da ya faru da daraktan nasa na kamfen, ya zargi EFCC da tsallake iyakar aikinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan da ya zanta da manema labarai bayan kada kuri’arsa GSS Gbajumba a karamar hukumar ta Guma, ya ce N100,000 ba wani kudin a zo a gani bane da zai iya jan hankalin masu kada kuri’u.

Saboda haka, gwamnan ya yi kira ga hukumar da ta gaggauta kame Tyokaa saboda ci gaba da rike shi daidai yake da take hakkinsa.

Ya kuma zargi hukumar da yiwa wata jam’iyyar siyasa aiki a jiharsa ta Benue, Punch ta ruwaito.

Na ji dadi da yadda aka fito yin zabe

A bangare guda, gwamnan ya bayyana jin dadinsa da yadda mutane suka fito don kada kuri’unsu a rumfuna 20 da INEC ta shirya a GSS Gbajumba.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso Za Su Raba Kuri’u Miliyan 87 Nan da Awa 24

Gwamnan, wanda ya kada kuri’arsa tare da matarsa Eunice ya ce mutanen jiharsa, musamman Benue North West na goyon bayansa, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa, yana da kwarin gwiwar lashe zaben da aka yi, a neman zama sanata da

Ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta bisa shirya zabe na gaskiya ba tare da muna-muna ba.

Gwamna Ortom dai na daga cikin wadanda suka bayyana goyon bayansu ga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour.

Asali: Legit.ng

Online view pixel