Shekara 7 da Rasuwarsa, Amurka ta Dawo da Miliyoyin Dalolin da Tsohon Gwamna Ya Sace

Shekara 7 da Rasuwarsa, Amurka ta Dawo da Miliyoyin Dalolin da Tsohon Gwamna Ya Sace

  • Kasar Amurka ta amincewa a dawowa Najeriya da wasu Daloli da Deprieye Alamieyeseigha ya boye
  • Marigayi Alamieyeseigha ya ajiye kusan $1m da ya wawura daga baitul-malin jihar Bayelsa a lokacinsa
  • ‘Dan siyasar ya yi Gwamna na tsawon shekaru kafin a same shi da laifin rashin gaskiya a kasar waje

America - Kasar Amurka da Najeriya sun shiga yarjejeniya domin dawowa gwamnatin kasar $954, 000 da Marigayi Deprieye Alamieyeseigha ya sata.

Jaridar Premium Times ta ce gwamnatin Najeriya za ta karbi wadannan makudan kudi da tsohon Gwamnan jihar Bayelsa da ya rasu ya boye su kasar waje.

Fahimtar da ke tsakanin kasashen nan ya jawo gwamnatocin Birtaniya da Amurka suka karbe duk wasu kadarori da dukiyoyin da 'Dan Najeriyan ya mallaka.

A wajen sa hannu a yarjejeniyar a ranar Alhamis a garin Abuja, Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Leonard tayi bayanin yadda za ayi amfani da wadannan kudi.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Ina za a kai kudin?

Misis Leonard ta ce an ware kudin wajen inganta harkar kiwon lafiya a Bayelsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A dalilin yarjejeniyar yau, za a bunkasa asibitocin da ake da su a Bayelsa ta hanyar gyara, samar da kayan aiki a dakunan shan magani kamar yadda jihar ta bukata."

- Mary Leonard

Buhari
Buhari a jirgin sama Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wanene Deprieye Alamieyeseigha?

Deprieye Alamieyeseigha ya yi mulki tsakanin 1999 da 2005 a jihar da ke Kudu maso kudancin kasar nan, daga baya sai aka yi ram da shi a birnin Landan.

A dalilin haka majalisar dokokin Bayalesa ta tsige shi, kuma aka yi shari’a da shi a kotu.

A daf da karshen shekarar 2015 tsohon Gwamnan ya rasu, amma kafin nan Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yafewa ‘dan siyasar laifuffukansa.

Wani rahoto da aka samu a gidan talabijin na Channels ya ce an yi bikin yarjejeniyar dawo da wadannan kudin sata ne a ma’aikatar shari’a ta tarayya a jiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

Jakadar Amurkar ta ce albashin Marigayin a lokacin yana Gwamna bai wuce $81, 000 a shekara ba, amma ya tara dukiya ta hanyar sata da sabawa doka.

Haduwarmu da Tinubu - Nyesom Wike

An ji labari Bola Tinubu, Kashim Shettima, Abdullahi Adamu sun ziyarci Nyesom Wike a Ribas tare da Atiku Bagudu, Babajide Sanwo-Olu, da David Umahi.

Kayode Fayemi, Timipre Sylva da Tony Okocha su na nan Gwamnan na Ribas ya fadi amanar da Tinubu ya rikewa Muhammadu Buhari a lokacin zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel