Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

Rotimi Akeredolu yana ganin tsarin sauya takardun kudi ya karawa jam’iyyar APC bakin jini

A yayin da zaben 2023 ya karaso, Gwamnan jihar Ondo ya bukaci ayi watsi da tsarin canza kudi

Gwamna Akeredolu ya koka kan yadda aka bar Godwin Emefiele a kan kujerar Gwamnan CBN

Ondo - A ra’ayin Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu yunkurin canza takardun kudi da gwamnati tayi, ya kawowa jam’iyyar APC bakin jini ne.

Ganin zabe ya gabato, Premium Times ta rahoto Gwamna Rotimi Akeredolu yana sukar canza kudi, ya bukaci a umarci CBN ya soke wannan tsari.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a jiya lokacin da ya zauna da matasan jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Seyi Tinubu a gidan gwamnati da ke Akure.

Rotimi Akeredolu ya yi kira ga shugaban kasa ya kyale mutane suyi amfani da tsofaffin da sababbin kudin tare musamman tun da kotu tayi hukunci.

Kara karanta wannan

Tattaunawa: Lauya Ya Shawarci INEC Kan Yadda Zasu Dakile Sayen Kuri'u

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto Akeredolu yana mai cewa ba a fito da tsarin a lokacin da ya dace ba, kuma ganin ana wahalar man fetur, hakan ya karawa APC rashin karbuwa.

Gwamnan APC
Shugaban kasa da Gwamnan Ondo Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Akwai matsala inji Gwamna

"Mu na fuskantar matsala a kasar nan a yau. Jam’iyyarmu ba ta da wani farin jini sosai.
Ka da mu yaudari kan mu. Dole ne sai yanzu za a fito da wannan tsarin tattaliin arziki? Ta ina? Ga sha’anin fetur ga komai? Abubuwa sun yi wuya."
Wannan tsari a yanzu bai zo a lokacin da ya kamata ba. Ya kamata a soke shi. A fadawa CBN a soke shi, a bari ayi amfani da sabo da tsohon kudi.
‘Yan acaba da bankuna ba su karbar tsohon kudi. Kotu ta ce a dakata amma kamar ba ayi ba. Mun ce tun farko a tsige mutumin nan (Gwamnan CBN)."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Caccaki Emefiele, Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Ya Sanya Ya Sauya Fasalin Kuɗi

- Rotimi Akeredolu

Ayi waje da Gwamnan CBN - Akeredolu

Akeredolu ya ce tun da Godwin Emefiele ya yi yunkurin samun takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya bada shawarar a sauke shi daga mukaminsa.

Gwamnan yake cewa Emefiele bai cancanci ya zama Gwamnan CBN ba, kuma zai kawo masu cikas. This Day ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Gwamnoni ba su yarda ayi sulhu ba

A wani rahoto, ta bakin Gwamna Nasir El-Rufai kun ji dalilin Gwamnonin Jihohi na kin yin sulhu da Gwamnatin tarayya a kan shari’ar canjin Nairori.

Nasir El-Rufai ya ce gwamnati ta na so cigaba da aiki da tsohuwar N200 kadai a matsayin kudi zuwa Afrilu, amma sun lura babu gaskiya a lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel