Ba Za a Yi Amfani da CBN Wajen Kawo Cikas Ga Zaben 2023 Ba, Inji Gwamnan Babban Banki Emiefele

Ba Za a Yi Amfani da CBN Wajen Kawo Cikas Ga Zaben 2023 Ba, Inji Gwamnan Babban Banki Emiefele

  • Gwamnan CBN ya ce ba za a yi amfani da bankin ba wajen kawo tsaiko ga zaben 2023 da ke tafe ba
  • Ana zargin CBN da sauya kudin Najeriya tare da sanyasu su yi karanci don kawo tsaiko ga zaben 2023
  • Jama'ar Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi, lamarin da ke jawo cece-kuce a kasar

FCT, Abuja - Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya bayyana cewa, ba za a yi amfani da bankinsa ba wajen kawo tasgaro ga zaben 2023 ba.

Emefiele ya bayyana hakan ne lokacin da shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmud Yakubu ya kai masa ziyara a CBN a ranar Talata 7 Faburairu, 2023, The Nation ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa, CBN zai samar da dukkan adadin tsabar kudade da INEC ke bukata don gudanar da aikin zabe cikin tsanaki.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Ya Sa Labule Da Gwamnan CBN Saboda Karancin Takardun Naira

Gwamnan CBN ya magantu kan zaben 2023 da karancin kudi
Ba Za a Yi Amfani da CBN Wajen Kawo Cikas Ga Zaben 2023 Ba, Inji Gwamnan Babban Banki Emiefele | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Shin CBN za ta kawo tsaiko ga zaben 2023?

Maganarsa martani ne ga bukatar shugaban INEC na cewa, ya kamata CBN ya kawo karshen karancin kudi da ake fama dashi a hannun jama’a, kwanaki 17 kafin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, ya ce:

“CBN ba zai bari a yi amfani shi a matsayin wakulin dagula zabe mai zuwa ba wanda aiki ne mai kyau da ke gaba.”

Shugaban na INEC ya shaidawa gwamnan CBN cewa, zaben 2023 zai kasance zabe mafi inganci a tarihi, inda ya kara da cewa, amma akwai batutuwan masu sarkakiya game da zaben.

Wasu 'yan siyasa a kasar nan na cewa, an kawo batun sauya fasalin kudi da ka'idarsa ne saboda kawo tsaiko ga zaben 2023 da ke tafe nan ba da dadewa ba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Toh fah: Makiyin Najeriya ne zai kawo batun sauyin kudi yanzu, inji dan takarar shugaban kasa

A kan talaka zai kare: El-Rufai ya damu da batun sauya fasalin Najeriya

A wani labarin, kun ji yadda gwamnan jihar Kaduna ya bayyana gaskiyar abin da ke ransa game da sauya fasalin Naira da CBN ya yi a shekarar nan.

El-Rufai ya bayyana tsoron cewa, dukkan wannan sauyin kudi a kan talaka zai kare, domin ba a ba talakawa sabbin kudi a bankunan kasar nan.

Ya kuma shaida cewa, masu kudi da 'yan siyasa na samun kudin, wani gwamna ya samu sabbin kudi na N500m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel