Atiku Ya Sanar da Sarkin Kano Abin da Ado Bayero Ya Taba Fada Masa a Kan Mulkin Najeriya

Atiku Ya Sanar da Sarkin Kano Abin da Ado Bayero Ya Taba Fada Masa a Kan Mulkin Najeriya

  • Atiku Abubakar ya kai ziyarar ban girma da neman albarka wajen Mai martaba Aminu Ado Bayero
  • ‘Dan takaran ya ce Alhaji Ado Bayero ya taba nuna masa cewa zai yi mulki a lokacin yana Sarkin Kano
  • Wazirin Adamawa ya nemi Sarki Aminu Ado Bayero ya yi masa addu’a domin cika burin mahaifinsu

Kano - Dinbin magoya bayan Atiku Abubakar sun nuna kan su a a garin Kano ranar Alhamis da ‘dan takaran shugaban kasar a PDP ya kawo ziyara.

Tribune ta rahoto cewa Atiku Abubakar da mutanensa sun yi kamfe a jihar Kano, kuma sun kai ziyara zuwa fadar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Wazirin Adamawa ya shaidawa Mai martaba cewa mahaifinsu watau Marigayi Ado Bayero ya taba fada masa cewa zai rike shugabancin Najeriya.

Atiku Abubakar yake cewa Ado Bayero wanda ya rike sarautar Kano tsakanin 1966 zuwa 2014 ya shaida masa wannan ne da ya taba ziyartar fadarsa.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

Ado Bayero ya hango shugaban gobe

"Mun kawo ziyarar ban girma zuwa fadar a baya, a lokacin ina mataimakin shugaban kasar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarki a lokacin, Ado Bayero ya fada cewa a cikinmu ya hangi wanda zai zama shugaban kasa, kuma zai kawowa Najeriya abubuwa na cigaba.
Atiku da Sarkin Kano
Atiku a fadar Sarkin Kano Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Ado Bayero bai tsaya nan ba, sai da ya yi addu’a wanda yake ganin zai yi mulki ya kawo gyara, ya inganta halin zamantakewa da tattalin arziki.”

- Atiku Abubakar

Atiku ya nemi tabarrukin Sarkin yau

‘Dan takaran na PDP yana ganin shi ne wanda Sarki Ado Bayero yake nufi a lokacin, don haka ya nemi Mai martaba Aminu Ado Bayero ya yi masa addu’a.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce idan Sarkin na yanzu ya yi masa addu’a, hakan zai iya sanadiyyar da burin mahaifinsu da ya bar Duniya zai cika.

Kara karanta wannan

Abin da Zai Faru Idan Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa a 2023 – Gwamnan APC

A kauracewa siyasar gaba - Aminu Ado Bayero

Yayin da ‘dan takaran ya gama neman albarka, Vanguard ta ce Aminu Ado Bayero ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji nuna bakar gaba wajen neman mulki.

Sarkin na birnin Kano ya bukaci masu takarar shugabanci da su rika bin ka’ida da dokokin kasa.

"Abubuwa sun juya a Kano"

Domin samun karin haske, Legit.ng Hausa ta zanta da Adnan Mukhtar T/Wada wanda ya shaida mana farin jinin Atiku ya karu sosai yanzu a Kano.

Hadimin na Shugaban masu yakin takarar Atiku Abubakar, Ibrahim Little ya ce tsarin canza kudi ya jawowa jam'iyyar APC bakin jini sosai a yanzu.

Adnan T/Wada ya ce da farko ana tunanin PDP tana bayan NNPP da APC a babban zabe, amma yanzu sun fara hango nasara a takarar shugaban kasa.

Tinubu ya jawowa Buhari zagi

A rahoton da mu ka fitar a baya, an ji yadda Atiku Abubakar ya zama Lauyan Muhammadu Buhari, Gwamnan CBN da Ministan shari’a da ‘Yan APC ke zagi.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Kwankwaso Zai Janye Wa Atiku Takara? Sabbin Bayanai Sun Fito Ana Gab Da Zaben 2023

Ganin mukarraban 'dan takaran APC, Bola Tinubu , su na ta caccakar Gwamnati mai-ci, Hadimin Atiku ya ce ya kamata Festus Keyamo ya rabu da kwamitin kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel