Buhari Ya Karbi Emefiele a Aso Rock Bayan Umarnin Kotun Koli Kan Batun Kudin Najeriya

Buhari Ya Karbi Emefiele a Aso Rock Bayan Umarnin Kotun Koli Kan Batun Kudin Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da gwamnan CBN jim akdan bayan hukuncin kotu kan sabbin kudi
  • Kotun koli ya hana CBN tabbatar da wa'adinsa na ranar 10 ga watan Faburairu don daina amfani da sabbin kudi
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar karancin sabbin kudi tun bayan sanya wa'adin daina amfani da tsoffin Naira

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a fadarsa, Aso Rock da ke Abuja, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan da kotun koli ta ta yi hukunci a ranar Laraba don yin watsi da wa'adin 10 ga watan Faburairu na daina amfani da tsoffin kudi.

Tawagar alkalai bakwai na kotun karkashin jagorancin mai shari'a John Okoro ne suka yanke hukunci kan karar da gwamnatocin Kogi, Kaduna Zamfara suka shigar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan Hukunci Kotun Ƙoli, IMF Ya Aike da Muhimmin Sako Ga CBN Kan Sabbin Kuɗi

Gwamnan CBN ya gana da Buhari bayan hukuncin kotun koli
Buhari Ya Karbi Emefiele a Aso Rock Bayan Umarnin Kotun Koli Kan Batun Kudin Najeriya | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Kotun kolin ta ce, gwamnatin tarayya da CBN dole su dakatar da batun daina amfani da tsoffin kudi har zuwa lokacin da kotun za ta sake duba batun a ranar 15 ga watan Faburairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya zuwa yanzu dai Legit.ng Hausa bata iya gano abin da shugaban ya tattauna da gwamnan na CBN akai ba, amma ana kyautata zaton batun sauya Naira ne.

'Yan Najeriya da sabbin Naira

Idan baku manta ba, rahotanni sun bayyana yadda 'yan Najeriya ke fama da karancin sabbin kudi a bankunan kasar nan.

Wannan ya kai ga suke siyan kudade tsoffi da sabbi a hannun wasu mutane kan farashin da ya saba doka da ka'idar kudi ta Najeriya.

Babban bankin Najeriya ya dage cewa, a halin yanzu akwai kudi a kasa, amma bankuna sun ki rabawa mutanen kasar nan.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Kolin Kan Naira: Tinubu Ya Jinjinawa El-Rufa'i, Matawalle da Bello Kan Shigar Da Buhari Kotu

Gwamnoni sun kai kara kotu

A tun farko, gwamnonin jihohin Arewa uku na APC ne suka maka gwamnatin Buhari a kotu don nemawa al'ummarsu mafita.

A cewar rahotanni, gwamnatocin Kogi, Zamfara da Kaduna sun garzaya kotu don kalubalantar wa'adin da CBN ya sanya na daina amfani da tsoffin kudi a kasar.

Sai dai, a hukuncin da kotun koli ta yi a yau, an hana CBN tabbatar da wa'adin tare da sanya ranar ci gaba da jin sauraran kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel