A Samo Min Katin Zabena Ko Kuma a Daga Zaben 2023, a Bani N500m, Dan Jarida Ya Maka INEC a Kotu

A Samo Min Katin Zabena Ko Kuma a Daga Zaben 2023, a Bani N500m, Dan Jarida Ya Maka INEC a Kotu

  • Dan jarida a Najeriya ya maka INEC a kotu, ya ce dole a bashi katin zabensa ko kuma a dakatar da zaben 2023
  • Hakazalika, ya nemi a bashi diyyar N500m saboda kokarin haramta masa yin zabe a matsayinsa na dan kasa mai kishi
  • A halin da ake ciki, saura kwanaki kadan a yi zabe, ba kowa ne ya samu katin zabe don kada kuri’a ba

Abuja - Wani dan jarida mamallakin kafar labarai ta Swift Reporters, Adewole Kahinde ya maka hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a kotu kan gaza samo masa katin zabensa.

Bayanan da Kahinde ya nunawa Punch sun bayyana cewa, ya nemi a sauya rumfar zabensa daga Area 11 zuwa Nyanya a Abuja biyo bayan sauya matsuguni da ya yi.

Bayan ya ziyarci ofishin INEC, an ce masa ba zai yiwu a sauya rumfar katinsa ba kamar yadda ya nuna a takardar da hukumar ta bayar ba.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun koma kwana gindin ATM saboda tsananin rashin kudi

Dan jarida ya maka INEC a kotu kan gaza bashi katin zabensa
A Samo Min Katin Zabena Ko Kuma a Daga Zaben 2023, a Bani N500m, Dan Jarida Ya Maka INEC a Kotu | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A halin da ake ciki, kwanaki kadan ne suka rage a yi zaben shugaban kasa na 2023, kuma har yanzu akwai wadanda basu karbi katin zabe ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda ya sauya rumfar zabe amma ya gaza samun katinsa

A cewarsa:

“Na sauya rumfar zaben katina a watan Yulin 2022 daga Area 11 ta magamar Area 3 zuwa sabon mazauni na a Nyanya.
“Na duba a yanar gizo don tabbatar da an yi nasarar sauya mazaunin katina zuwa Nyanya kamar yadda ya bayyana a kafar yanar gizon INEC.
“Da naje ofishin INEC na Karu a karkashin AMAC, aka karbi takardar sannan na jira kusan sa’o’i 3, aka ce min ba a ga katina ba. Na cike wani fom aka ce na dawo bayan sati biyu.”

A cewarsa, bayan ya jira sati biyu, aka ce masa ba zai samu katin ba har ya zuwa yau.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Shekara 20 Mai Koyon Sana'a Ya Kashe Mai Gidansa, Ya Jefa Gawarsa Cikin Rijiya

Ya kuma shaida cewa, ranar Asabar 4 ga watan Fabrairu ne karo na bakwai da kai ziyarar duba katinsa a ofishin INEC amma bai samu ba.

Dole a bani diyya ko a dakatar da yin zabe

Bayan bin duk hanyar da zai bi don ganin ya samu katinsa amma abin ya gagara, sai ya yanke shawarin maka hukumar a kotu tare da neman a bashi diyyar N500m duk da kuwa kuri’a daya ta fi darajar hakan.

Da yake karin bayani kan karar da ya shigar, ya ce:

“Akwai dubban ‘yan Najeriya da suka nuna sha’awar shiga sahun karar da na shigar kan INEC, kuma idan aka yi sa’a a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, lauyana zai kai batun ga INEC.
“Ko dai INEC ta bani katin PVC na kafin 25 ga watan Fabrairun 2023, ko kuma kotu ta dakatar da yin zabe har sai an ciro katina na PVC an bani a hannu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ankarar da Magoya-Baya a Kan Sirrin Jawo Wahalar Fetur da Karancin Nairori

“INEC bata isa ta hana ni kada kuri’a ba kuma ba zan yi zabe da tsohon PVC ba tun da an riga an mai dani Nyanya.”

INEC dai a baya ta ce bata tunanin dage zabe a 2023 ba, don haka kowa ya shirya kada kuri'a a zaben mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel