Tinubu Ya Ankarar da Magoya-Baya a Kan Sirrin Jawo Wahalar Fetur da Karancin Nairori

Tinubu Ya Ankarar da Magoya-Baya a Kan Sirrin Jawo Wahalar Fetur da Karancin Nairori

  • Da ya je kamfe a Ekiti, Asiwaju Bola Tinubu ya soki tsarin da bankin CBN ya fito da shi a kaikaikce
  • ‘Dan takaran ya ce an kirkiro karancin takardun kudi ne domin kurum a fusata mutanen Najeriya
  • Bola Tinubu yake cewa idan jama’a su ka ji haushi har suka tada rigima, za a janye zabe mai zuwa

Ekiti - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ce an jawo wahalar man fetur da takardun kudi ne saboda a daga zabe.

A yammacin Juma’a, Punch ta rahoto Asiwaju Bola Tinubu yana cewa an boye takardun sababbin kudi ne domin a fusata mutane har a jawo rigima.

‘Dan takaran ya ce burin masu wannan nufi shi ne barke da rikici ta yadda za a dakatar da zabe, a dalilin hakan sai a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Jaridar ta ce tsohon gwamnan na Legas ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da ya je yawon yakin neman zabensa a Ekiti Parapo Pavilion a jihar Ekiti.

Saboda ku na ke takara - Tinubu

A jawabin da ya yi a garin Ado Ekiti, ‘dan siyasar ya shaidawa mahalarta taron kamfensa cewa yana takara a APC ne saboda ya nema masu mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin halin da aka shiga ciki a kasa a yau, The Cable ta rahoto Tinubu yana cewa ana kokarin fusata al’umma ne ta yadda za a kai ga yin rigingimu.

Tinubu
Bola Tinubu a Ekiti
Asali: Facebook

‘Dan takaran yake cewa ba za su biyewa wannan makarkashiya ba, ya yi kira ga mutanen jihar Ekiti su hakura su kada kuri’arsu ranar zabe a kafa.

“Su na boye Naira ne saboda ku fusata, ku yi fada. Su na neman jawo hatsaniya saboda a daga zaben, abin da suke so shi ne gwamnatin rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Mun fi su wayau. Ba za muyi fada ba. Duk beran da ya ci guba, kan shi zai kashe.
Ina takarar ne saboda in gyara rayuwar mutane. Idan saboda abin da zan ci ne, Ubangiji ya azurta ni. Ina takara ne domin in gyara rayuwarku tayi kyau.
‘Yan Ekiti mutane ne masu ilmi sosai. Sun yi karatu a kyau; ba su wasa da ilmi. Amma bai dace a gama karatu babu aiki ba, za mu nema maku ayyukan yi.
Ranar zabe za mu taka da kafa zuwa filin zabe domin mu kada kuri’armu. Rumfunan zabenku ba su da nisa da inda ku ke zama, don haka ku je da kafa.”

- Bola Tinubu

Dalilin duba albashi - RMAFC

A yayin da ake fama da wahalar canjin kudi, an ji labari ana kokarin kara albashin da ake biyan shugaban kasa, mataimakinsa da kuma Ministocin tarayya.

Canjin da RMAFC zai yi zai shafi Gwamnoni, Mataimakan Gwamnonin jihohi, ‘Yan majalisar dokoki da na tarayyar har da Sanatoci masu ba su shawara.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Kuma Sukar Mulkin Shugaba Buhari a Gaban Jama’a Wajen Yawon Kamfe

Asali: Legit.ng

Online view pixel