Yan Najeriya Sun Koma Kwana Bakin ATM Saboda Tsananin Rashin Kudi

Yan Najeriya Sun Koma Kwana Bakin ATM Saboda Tsananin Rashin Kudi

  • Abu ya yi kamari a fadin tarayya inda mutane suka fara kwana bakin ATM don samun cire yan kudadensu
  • CBN ta ce kuma mafi akasarin kudin da mutum zai isa samu a rana shine Naira dubu ashirin kacal
  • Yan Najeriya sun nuna bacin ransu game da wahalar da aka jefasu ciki babu gaira babu dalili

Yan Najeriya na bayyana fushi da bacin ransu game da halin da karancin takardun kudin Najeriya, Naira, ya jefasu inda abin har ya kai wasu na kwana a gindin na'urar ATM.

Rahoton SaharaReporters ya nuna yadda wasu kwastamomi a jihar Enugu suka kai har karfe 2 na dare suna layin cire kudi a ATM.

Wasu suna zuwa tun misalin karfe 3 na dare zuwa wayewar gari saboda su kasance na farko a layi lokacin da banki ya bude karfe 8.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Bi Banki-Banki Yana Musu Barazanar Kullesu Idan Basu Fito Da Kudi Ba

An tattaro cewa su kansu bankuna basu zuba isassun kudi a na'urar ATM kuma doka ta ce mutum ba zai iya cire sama da N20,000 ba a rana.

Layin
Yan Najeriya Sun Koma Kwana Bakin ATM Saboda Tsananin Rashin Kudi Hoto: @Saharareporters
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jihar Sokoto, wani mutumi dan garin Wamako, Aliyu Muntari, ya bayyana Saharareporters cewa kawai ya yanke shawarar zuwa da yar katifarsa don ya cire N10,000."

A cewarsa:

"Tun da Wamakko na zo, yau kwana uku uku kenan cikin garin Sokoto. Da taburmata na shigo domin kwana a bakin ATM saboda ina son N10,000."
"Ba ni kadai bane, za ga mutane a wajen. Zamu kwana a nan sbaoda idan aka zuba kudin da safe, zamu iya cira."

Wani mutumi mai suna, Saminu Kurfi, ya ce:

"Duba irin halin da talakawa suka shiga, N1000 fa wani ke bukata domin sayen kayan abinci amma ba zaka samu ba."

Kara karanta wannan

Kaico: Rashin sabbin Naira ya kai ga mutuwar mata mai tsohon ciki a wata jihar Arewa

"Yanzu kusan dukkan kasuwanni musamman a karkara sun daina karban tsaffin kudi, kasuwanci yanzu ya gagara."

Wani bawan Allah, Oforbuike Moses, a jihar Enugu ya bayyanawa manema labarai cewa kwanansa uku yana zuwa banki amma hannu wayam yake komawa bai samu ba.

A cewarsa:

"Yau kwana na hudu kenan ina zuwa banki. Zan baro gidana karfe 4 na dare saboda in samu cire kudi. Amma da na isa ATM na First Banki a Okpara Avenue, sama da mutum 100 ke layi."
"Karfe 4 na dare amma nine lamba na 115. Mutum 114 sai sun rigani cire kudi."

Wani mutum mai suna Kingsley Obi ya bayyana cewa;

"Jiya karfe 1:30 na dare na tafi ciro N20,000 kacal, sai karfe 11 na samu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel