Yadda Dan Shekara 20 Mai Koyon Sana'a Ya Kashe Mai Gidansa, Ya Jefa Gawarsa Cikin Rijiya

Yadda Dan Shekara 20 Mai Koyon Sana'a Ya Kashe Mai Gidansa, Ya Jefa Gawarsa Cikin Rijiya

  • Wani matashi da ake zargin ya kashe mai gidansa da ke koya masa sana'a ya fada komar yan sanda a Ondo
  • Wata majiya ta bayyana cewa rikici ne ya shiga tsakanin sa da ogan nasa har takai ya fasa masa waya shi kuma garin mayar da martani yayi ajalinsa
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin tare alkawarin za a tura yaron kotu da zarar bincike ya kammala

Ondo - Rundunar yan sandan Jihar Ondo ta kama wani yaro dan shekara 20, Josiah Godwin, bisa zargin hallaka maigidan sa, Saviour Joseph, har lahira a yankin Imafon, Karamar Hukumar Akure ta Kudu da ke Jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wanda ake zargin, bayan ya kashe mamacin, ya kuma jefa gawarsa a wata rijaya kusa da inda suke aiki.

Kara karanta wannan

Magidanci ya Watsawa Matarsa Fetur Tare da Cinna Mata Wuta Saboda ta ki Masa Girki a Ogun

Yan sandan Najeriya
Yadda Dan Shekara 20 Mai Koyon Sana'a Ya Kashe Mai Gidansa, Ya Jefa Gawarsa Cikin Rijiya. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Yadda matashi dan shekara 20 ya halaka mai gidansa a Ondo

Wata majiya ta bayyana cewa rikicin ya fara ne tsakanin sa da mamacin, mai aikin rufi, wanda ya tarwatsa wayar yaron da ake zargi a kasa saboda wata hatsaniya inda shi kuma yaron ya farmake shi da niyar mayar da martani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, yayan mamacin, Mr. Odey Ogbaji, ya ce gawar mamacin mai shekaru 27 an tsince ta bayan kwana hudu a wata rijaya da ke kusa da inda shi mamacin da yaron nasa da ake zargi suke aiki.

Ya ce:

''Satin da ya gabata ranar Talata, dan uwana ya kira ni da safe munyi magana. Amma ranar Laraba, na gwada kiran shi bata shiga ba. Na dauka batirin wayarsa ne ya mutu, har sai ranar Asabar da na kira daya kanin nawa ya ke kuma yi min korafin rashin samun mamacin a waya.

Kara karanta wannan

Kaico: Rashin sabbin Naira ya kai ga mutuwar mata mai tsohon ciki a wata jihar Arewa

''Daga bisani, sai muka tuntubi yaron shi da suke aiki. Da suka samu yaron, sun tambaye shi ko ina maigidan sa ya shiga sai ya ce maigidan nasa ya tashe shi tsakar dare, ya karbi wayarsa, ya fasa ta a kasa ya kuma fara dukan shi sannan ya ce ya koma ya cigaba da bacci.
''Ya ce washe gari, ya yanke shawarar barin wajen aikin. To, sai muka tambaye shi ta yaya zai tashi da safe ba tare da ya ga maigidansa ba kuma ya bar wajen aiki. Sai ya ce wai a tunanin shi maigidan nasa yana bandaki lokacin da ya tafi.
''Da muka duba wayar da yace an fasa, ko kwarzane babu a jikinta''.

Martanin Yan Sanda

Jami'ar hulda da jama'a na rundunar yan sandan Jihar, Mrs Funmiloya Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da tabbatar da kama wanda ake zargi.

Ta ce:

''Yaron ya fusata, ya kashe maigidansa ya kuma jefa gawarsa a rijiya. A mayar da batun gaban sashen binciken manyan laifuka na CID kuma da zarar an kammala bincike za a tura shi kotu.''

Kara karanta wannan

Fasto Ya Yada Labarin Karya Cewa Ya Mutu Gudun Kada Ya Biya Bashin N3m

Wani mazaunin Abuja ya halaka abokinsa ya birne gawarsa saboda rikici kan kudi

A wani rahoton, yan sanda sun kama wani mutum dan shekara 63 mazaunin Abuja, Taiwo Ojo, kan zarginsa da halaka abokinsa mai suna Philip Kura.

Rahotanni sun bayyana cewa Ojo ya buga wa Philip shebur ne a kansa yayin da suke jayayya kan wani kudi sannan ya janye gawarsa ya boye a cikin wani dan karamin daji, daga bisani ya birne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel