Ana Karancin Sabbin Naira a Banki, Wasu Mutane Na Tallarsu a Cikin Tasha a Zaria

Ana Karancin Sabbin Naira a Banki, Wasu Mutane Na Tallarsu a Cikin Tasha a Zaria

  • Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan karancin sabbin kudi, an ga wasu mutane na siyar da kudi a kasuwa
  • Wani wanda ya siya kudi ya bayyana yadda ya siya kudi N20,000 a kan farashin N25,000 a jihar Kaduna
  • Babban bankin Najeriya ya dage wa’adin da ya sanya na daina amfani da tsoffin kudi a kasar

Zaria, jihar Kaduna - A daidai lokacin da ake fuskantar karancin sabbin Naira a Najeriya, an ga wasu mutane suna tallansu a tashar Dadi da ke Sabin Gari a birnin Zaria ta jihar Kaduna.

A cewar rahoton da muka samo, masu tallar kudin na karbar kari mai yawa kan adadin sabbin da suke ba mai bukata, Vanguard ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ce ya ga damin kudade da yawa da ake tallarsu tsirara a tashar ta Dadi da ke yankin Kwangila a Zaria.

Kara karanta wannan

Yadda Ake Siyar da Sabbin Kudi a Fitacciyar Tashar Zaria, Ana Zabga Riba ga Jama'a da Suka Matsu

Ana dillancin sabbin Naira a Arewa
Ana Karancin Sabbin Naira a Banki, Wasu Mutane Na Tallarsu a Cikin Tasha a Zaria| Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

An gano cewa, ana siyar da daurin N200 a kan N30,000, daurin N5000 a kan N70,000, N1000 a kan N130,000 da kuma N100 a kan kudi N16,000.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Malam Muhammad Bello, wani mai tallan sabbin kudi ya sahida cewa, sukan biya N70,000 zuwa N130,000 don samun N500,000, ya danganta da darajar kudi.

Sai dai, Bello ya ki bayyana gaskiyar inda suke samun sabbin kudaden da kuma yadda suke samu ba.

Yadda wani ya siya N20,000 a farashin N25,000

Mr. Thomas Damina, wani mazaunin kauyen Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina da ya siya kudin ya tabbatar da cewa, ya siya sabbin ‘yan N1000 na N20,000 a kan kudi N25,000.

Ya ce ya siya kudin ne a Zaria saboda ya matsu domin biyan leburorin da suka yi masa aiki a gonarsa ta noman rani, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

A cewar Damina:

“’Yan kasuwa a kauyenmu (Gozaki) ba sa karba tsoffin kudi kuma babi sabbin a banki. Bani da zabin da ya wuce na siya a wurin masu talla.”

An gano cewa, bakar kasuwar sabbin kudade na ci sosai, domin mutane da yawa na siyan kudaden don kujewa asarar kudi yayin da wa’adin CBN ke kara matsowa.

Babu kudi a ATM

A lokacin da aka majiya ta ziyarci bankunan kasuwanci da ke yankin PZ a Zaria, babu injin ATM da ke ba da kudi.

Harkallar siyar da kudin Najeriya dai ya saba da dokar CBN sashe na 21, 2007, kuma abin hukuntawa ne daidai da sashe na 21 sakin layi na 4 a dokar.

Duk da tanadin doka, dillalai da ke tallan sabbin kudaden na yawo a kasuwar Sabon Gari a Zaria ba tare da buya ko tsoron kamu ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige ya ce, ‘yan sanda za su yi bincike don kamo masu aikata wannan laifin.

Kara karanta wannan

Cikin sauki: Yadda za ku yi ku rabu da tsoffin Naira, ku sami sabbi a kusa daku

Ana tsaka da jira, babban bankin kasa ta sanar da dage wa’adin daina amfani da tsoffin kudin zuwa watan Fabrairun bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel