CBN Ya Tsawaita Lokacin Amfani da Tsohon Kudi, An Bada Sabon Wa’adi a Najeriya

CBN Ya Tsawaita Lokacin Amfani da Tsohon Kudi, An Bada Sabon Wa’adi a Najeriya

  • A yau Babban bankin Najeriya ya sanar da cewa an canza lokacin daina karbar tsofaffin kudi
  • A wata sanarwa da Godwin Emefiele ya fitar, ya ce takardun za su cigaba da amfani har Fubrairu
  • Bayan an yi sababbin N200, N500 da N1000, CBN ya tattaro tsofaffin N1.9tr, saura N900bn suka rage

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN ya tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun Naira a matsayin kudi a Najeriya.

Gwamnan CBN na kasa watau Godwin Emefiele ya bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ya sa wa hannu a safiyar Lahadin nan.

Gidan talabijin Channels ya rahoto Mista Godwin Emefiele yana cewa za a cigaba da amfani da tsofaffin kudin na karin kwana goma.

Sai ranar 10 ga watan Fubrairun 2023 za a daina karbar takardun a matsayin kudin Naira.

Kara karanta wannan

Muna goyon bayan kira ga dage ranar daina amfani da tsaffin kudi, Shugabannin bankuna a Najeriya

Gwamnan CBN
Buhari da Gwamnan CBN Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin fadar Shugaban kasa

Mai taimakawa shugaban Najeriya a harkar kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad, ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter.

Da yake bayani a ranar 29 ga watan Junairu 2023, Ahmaad ya ce Godwin Emefiele ya sanar da karin wa’adin zuwa Fubrairu mai zuwa.

Daily Trust ta ce a cikin watanni uku, an yi nasarar maida fiye da rabi na tsofaffin kudin da aka buga zuwa asusun babban banki.

“Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin kudi har sai 10 ga watan Fubrairu.
Godwin Emefiele ya sanar da karin wa’adin a wani jawabi da ya sa wa hannu a ranar Lahadi.
Gwamnan babban bankin na Najeriya ya ce zuwa yanzu CBN ya karbi Naira Tiriliyan 1.9 na tsofaffin kudi.
Zuwa yanzu akwai ragowar Naira biliyan 900 da suka rage a hannun mutane kafin a cin ma manufar tsarin.”

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gwamnan CBN ya ki zuwa majalisa kan batun sabbin Naira, kakaki ya fadi matakin da zai dauka

NigeriaGov ta ce daga 10 ga watan Fubrairu za a daina amfani da kudin, sannan daga ranar 17 ga watan ne za a daina canza su a bankuna.

Muhammadu Buhari ya amince da karin ne bayan ya zauna da Gwamnan CBN. Rahotanni sun ce an yi zaman ne a Daura, jihar Katsina.

Kiran da El-Rufai ya yi

A wani rahoto da muka fitar, an ji Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin CBN da ya kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudi.

Gwamnan na jihar Kaduna ya ce mutanen karkara ne wa’adin CBN zai fi yi wa illa, ya ce mutanen da ke kauyuka sun yi nesa da bankuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel