Bakar Kasuwa: Yadda Ciniki Ya Budewa Masu Siyar da Sabbin Kudi a Zaria

Bakar Kasuwa: Yadda Ciniki Ya Budewa Masu Siyar da Sabbin Kudi a Zaria

  • Karancin sabbin kudi yana cigaba da janyo karuwar masu kasuwancin sabbin kudin kan farashi mai tsadar gaske a gari
  • Bincike sun nuna yadda wasu masu tallar sabbin kudi a tashar motar Dadi na Sabon Garin Zaria da ke jihar Kaduna suka yi dandazo a gefen babban titin suna tallata hajarsu
  • An tattaro yadda a yanzu suke siyar da bandir din 'yan N200 kan N30,000; bandir din 'yan N500 kan N70,000 da kuma bandir din 'yan N1000 kan N130,000

Zaria, Kaduna - Ana tsaka da karancin sabbin kudi, masu tallar sabbin kudin da aka canza sun cika tashar motar Dadi da ke karamar hukumar Sabon Garin Zaria da ke jihar Kaduna.

Sabbin kudi
Bakar Kasuwa: Yadda Ciniki Ya Budewa Masu Siyar da Sabbin Kudi a Zaria. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, wadannan masu tallar suna siyar da sabbin kudi kan farashi mai tsadar gaske.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Babban bankin Najeriya ya tsaya kan bakarsa na cewa babu gudu ba ja da baya kan wa'adin daina amsar tsoffin kudi.

Bincike ya bayyana yadda masu tallar sabbin kudi daban-daban daga bandir din 'yan N100 da suke saidawa kan N16,000, N200 wanda suke siyarwa N30,000 duk bandir daya; bandir din N500 kan N70,000 yayin da suke siyar da bandir din N1000 kan N130,000.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ke faruwa

Yayin labarta yadda lamarin ya auku, wani mai tallar sabbin kudi, Muhammad Bello ya ce yana siyan bandir na sabbin 'yan N500 kan N70,000 zuwa N130,000.

Yayin da aka bukaci ya fallasa yadda ya samu kudin, ya yi mursisi ya ki cigaba da bada bayanai kan harkallar tasu.

Sai dai, wani mazaunin kauyen Gozaki na karamar hukumar Kafur da ke jihar Katsina ya bayyana yadda ya siya N20,000 na 'yan N1000 kan N25,000.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Karba Kudin da Zasu Zama Takardun Tsire ba: 'Yan Bindiga Sun ki Karbar Tsofaffin N5.3m na Fansa a Kaduna

Mutumin wanda ya ce sunansa Damina ya bayyana yadda bashi da wani zabi da ya wuce ya siya sabbin kudin kan farashi mai tsada saboda yana so ya biya laburorin da ke masa aiki a gonarsa.

A cewarsa:

"Masu siye da siyarwa a yankina (Gozaki) suna kin amsar tsoffin kudi kuma babu sabbin kudi a bankuna. Bani da wani zabi da ya wuce in siya daga masu hada-hadar kasuwancin sabbin kudin."

Haka zalika, bincike ya bayyana yadda kasuwancin sabbin kudin ke matukar ci a Zaria ga mazauna yankin, 'yan kasuwa da sauran masu saide-saiden kayayyaki don cimma wa'azin karbar kudin CBN na 31 ga watan Janairu.

Sai dai har ila yau an tattaro yadda wasu bakunan cikin gari a Zaria na jihar Kaduna suka daina bada kudi.

Doka ta haramta siyar da kudi kuma laifin ne da ke da daukar horo kamar yadda yazo a sashi na 21 sakin layi na 4 a kundin dokar CBN na 2007.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mabarata Sun Dire Gefe, Sun Daina Karbar Tsofaffin Takardun Naira

Duk da dokar ta bayyana karar hukuncin wannan dabi'ar, bai hana masu tallar keta dokar CBN ba gami da cin kasuwarsu wanda basa da nisa da 'yan sanda a Kwangila na Sabon Garin Zaria.

Legit.ng Hausa ta binciki lamarin inda wata matar aure da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa:

"Dama can wurin ana siyar da kudi sabbi. Ni idan za ni biki tashar nake zuwa in yi canjin kudi amma farashin bai haura kamar na yadda yanzu suke siyarwa ba.
"Wata makwabciyata 'yar kasuwa ta rasa yadda za ta yi. Tana fita aiki shiyasa ba za ta iya zuwa bin layin banki ba. Daya daga cikin masu siyar da kudin ta nema ya canza mata kudinta. Sai dai bata bayyana min a yadda farashin yake ba.

Yayin martani ga labarin nan, kakakin 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige ya bayyana yadda jami'an 'yan sandan suka gaggauta daukar mataki don kawo karshen mummunar harkallar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel