Hanyoyin da Za Ku Iya Bi Don Rabuwa da Tsoffin Kudaden Naira, Ku Sami Sabbi

Hanyoyin da Za Ku Iya Bi Don Rabuwa da Tsoffin Kudaden Naira, Ku Sami Sabbi

  • Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da shiga tsoro saboda karancin sabbin Naira, CBN ya ba da mafita
  • Akwai hanyoyi biyu da 'yan Najeriya za su bi don samun sabbin kudade tare da maida tsoffi zuwa bankunan kasar
  • A baya rahotanni sun bayyana yadda CBN ke gargadi ga 'yan Najeriya kan su gaggauta mayar da tsoffin kudi banki

Najeriya - Najeriya Yayin da wa’adin CBN ke kara gabatowa, ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da halin da za su shiga kan samun sabbin kudi.

Hakazalika, wasu da dama na kokawa kan halin da bankuna ke jefa mutane na karancin kudade da kuma dogayen layuka da ake samu a bankuna.

CBN ya ce akwai kudi a banki, amma bankunan Najeriya na kasuwanci sun ki zuwa dauka don rabawa ‘yan kasar a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Gwamnan PDP a Arewa bai taba ganin sabbin Naira ba, ya tura sako ga Buhari

Yadda za a rabu da tsoffin kud
Hanyoyin da Za Ku Iya Bi Don Rabuwa da Tsoffin Kudaden Naira, Ku Sami Sabbi | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Ta yaya za ku rabu da tsoffin kudi kana ku samu sabbi? Rahoton da muka samo ya hada dukkan abubuwan da ake bukata don warware matsalar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za ku iya kai kudadenku banki, a ajiye ko a baku madadinsu

Duk mai rike da tsohon kudi zai iya amfani da bankin da ke kusa wajen sanya kudadensa a asusu kafin cikar wa’adin CBN.

Duk da haka, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da adadin kudin da za a iya bayarwa a banki ba.

A ka’idar da banki ta ta sanyam mutum ba zai iya karbar sama da N20,000 a kan kanta. Duk da haka, wannan hanyar dai ita ce hanya mafi sauki.

ATM zai iya ba ka kudin da ka ajiye a banki

A bangare guda kuma, akwai ATM, domin ana iya cire adadi mai yawa da ya haura N20,000 a injunan ATM a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Akwai matsala fa: Direbobi a wata jihar Arewa sun cije, sun fadi abin da suke so CBN ta yi

Abin da ya tabbata daga CBN dai shine, babu wariya babu raini, kowa zai iya kai kudinsa banki domin a ajiye masa a cikin asusu.

Mafi yawancin inda ‘yan Najeriya ke kokawa shine; su kawo tulin kudi tare da tsammanin a basu adadin da suka kawo a matsayin musaya.

Idan baku manta ba, an ba kowane dan Najeriya damar cire kudin da ya kai N500,000 a duk mako, kamfanoni kuma za su iya cire kudin da bai haura N5,000,000 ba.

Wakilin CBN za su bude muku asusu, ko su zuba muku kudadenku a bankinku

CBN ya ce ya kirkiri shirin musaya domin rage wahala ga mutanen da ke nesa ga bankuna wajen mayar da tsoffin kudade banki.

A ranar 23 ga watan Janairu ne CBN ya ce yana da agent-agent da ke a fadin kasar nan da ke kan aiki shigar da kudaden ‘yan Najeriya banki.

Tsarin agent-agent na CBN zai taimakawa mutanen kauye wajen shigar da kudadensu cikin sauki tare da rage bin dogayen layuka a bankuna.

Kara karanta wannan

Da walakin: CBN ya yi sabon batu game da karancin sabbin Naira da aka buga kwanan nan

Irin wakilan na CBN sun hada kamfanonin POS da masu hada-hadar kudade da walet-walet da dama da ake amfani dasu a fadin kasar.

Ta wannan tsarin, yana da matukar sauki ga mutumin kauye ya mallaki asusun banki tare da ci gaba da zuba kudi ko don gaba.

Dama CBN ya ce duk wanda aka ba tsohon kudi a banki to kada ya karba saboda hakan ya saba ka'idar da ake tafiya a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel