Batun Sabbin Kudi Ya Sa Majalisar Wakilai Ta Yi Barazanar Kama Gwamnan CBN Emefiele

Batun Sabbin Kudi Ya Sa Majalisar Wakilai Ta Yi Barazanar Kama Gwamnan CBN Emefiele

  • Majalisar wakilai ta yi barazanar tura sufeto janar na 'yan sanda ya kamo gwamnan CBN saboda ya ki zuwa a zauna dasu
  • Kakakin majalisa ya ce, doka ta bashi damar kwamushe kowa a Najeriya, don haka zai iya yin hakan ga gwamnan CBN
  • Ana neman Godwin Emefiele a majalisa don tattauna batun da ya shafi tsoffin kudi da karancin sabbi a bankunan kasar nan

FCT, Abuja -Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar amfani da tanadin kundin tsarin mulkin kasar nan; sashe na 89(D) don kwamushe gwamnan CBN tare da kawo shi gaban majalisar.

Sashen na 89 a kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba majalisa karfin ikon ba da umarnin kamu ga duk wanda ya gaza amsa gayyatarsa, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shikenan: A Madadin Korafi, Zulum Ya Samo Hanyar da 'Yan Jiharsa Za Su Rabu da Tsoffin Kudi

A jiya Laraba 25 ga watan Janairu, majalisar wakilai ta shirya zama da manyan masu ruwa da tsaki na CBN da shugabannin bankuna don jin ta bakinsu game da dalilin da yasa ake samun karancin sabbin kudade a bankunan kasar nan.

Kakakin majalisa zai dauki mataki kan gwamnan CBN
Batun Sabbin Kudi Ya Sa Majalisar Wakilai Ta Yi Barazanar Kama Gwamnan CBN Emefiele | Hoto: intelregion.com
Asali: UGC

Hakazalika, zaman an ce zai yi duba ga yiwuwar sake sanya sabon wa’adi ga daina amfani da tsoffin kudade da bankin na kasa ya buga a watan jiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa ake neman zama da gwamnan CBN

Idan baku manta ba, majalisar kasa ta nemi Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dage wa’adinsa na 31 ga watan Janairu zuwa karshen watan Yuli don ba kowa damar rabuwa da ala-ka-kai na tsoffin kudade.

Sai dai, gwamnan bai halarta ba, kana bai turo wakili zuwa zaman da aka shirya yi a jiya Laraba da misalin karfe 3 na yamma ba, wannan yasa aka sake tura zaman zuwa ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Baku isa ba ku karya kasa: Majalisa ta dura kan CBN game da sabbin Naira, ta fadi matakin da za ta dauka

A cikin wasikar da majalisar ta karanta a ranar Alhamis, mataimakin gwamnan CBN ya ce, Godwin Emefiele na daya daga cikin tawagar da aka tura zuwa birnin Dakar, kasar Senegal.

Kai abokina ne, amma zan sa a kama ka

Da yake martani ga CBN, Gbajabiamila ya ce, duk da cewa Emefiele abokinsa na kut-da-kut, shi da sauran mambobin majalisa na da ikon tankwara shi daidai da tanadin kundin tsarin mulki.

Ya ce gaskiya gwamnan CBN bai kyauta ba da ya gaza amsa gayyatar majalisar, kana ya ki turo wakili a irin wannan yanayi mai bukatar ujila, Punch ta ruwaito.

Ya ce matukar ganawarsu ta gagara ga kuma ‘yan Najeriya na fuskantar wahala, zai turasasa sufeto janar na ‘yans anda ya kamo gwamnan tare da kawo shi gaban majalisa.

A halin da ake ciki, wani gwamnan PDP ya ce bai taba ganin sabbin kudin da CBN ta buga ba, ya nemi a kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudi.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya rasu, wa zai maye gurbinsa? Ga abin da doka ta tanada

Asali: Legit.ng

Online view pixel