Muna goyon bayan majalisa game kira ga dage ranar daina amfani da tsaffin kudi, Shugabannin bankuna a Najeriya

Muna goyon bayan majalisa game kira ga dage ranar daina amfani da tsaffin kudi, Shugabannin bankuna a Najeriya

  • Ranar Alhamis kwamitin majalisar wakilai ta zanna da shugabannin bankuna a Najeriya
  • Majalisa ta gayyaci gwamnan CBN, Godwin Emefiele, amma yayi kunnen uwar shegu ga gayyatar
  • Gwamnatin shugaba Buhari ta ce tana kan bakanta, ba zata dage ranar daina amfani da Naira ba

Abuja - Mambobin majalisar wakilan Najeriya sun yi ganawa da shugabannin bankunan dake Najeriya kan lamarin sabbin kudin Naira da karewar wa'adin tsaffin kudi.

Kwamitin da majalisa ta nada na musamman ta shiga zaman da shugabannin bankunan ne ranar 26 ga watan Junairu, 2023.

TVC ta ruwaito cewa taron ya gudana ne a cikin daya daga cikin dakunan taron majalisar wakilai dake birnin tarayya Abuja.

Reps meeting
Majalisar Wakilai Sun Shiga Zama Da Shugabannin Bankunanan Najeriya Hoto:@tvcnewsng
Asali: Twitter

Shugabannin bankunan sun bayyana goyon bayansu ga mambobin majalisar wakilan game da kira ga a dage ranar daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kara Wa’adin Rufe Karbar PVC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun bayyana hakan bayan zamansu da yan majalisar, rahoton ya kara.

Daya daga cikin shugabannin bankunan, Hadiza Ambursa wacce ta wakilci Access Bank ta bayyana cewa abinda ya kamata shine suna karban kudi su zuba cikin na'urorin ATM.

Amma su kansu basu samun isassun kudin.

Hakazalika Shehu Aliyu daga First Bank ya ce ra'ayin yan majalisa na a dage ranar shine maganar gaskiya.

Kalli bidiyon:

Sabbin Naira: Gwamnan CBN ya ki zuwa majalisa don tattauna batun kudi, majalisa ta fusata

Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Mr Hakeem Femi Gbajabiamila ya fusata da gwamnan bankin CBN kan rashin biyayya ga sammacin da mambobin majalisar suka yi masa.

Gbajabiamila ya yi barazanar cewa zasu yi amfani da dokar kasar nan wajen kamashi karfi da yaji idan ya sake watsi da gayyatarsu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Na Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Cewar Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow

Kakakin majalisan ya ce sashe na 89(D) na kundin tsarin mulki ya basu damar gayyatar koma wanene kuma suna ikon sanya IG na yan sanda kwamushe mutum tare da kawo shi gaban majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel