Rashin Tsaro Ya Fatattaki ‘Dan Takaran Shugaban kasa, Ya Hana Shi Taro a Katsina

Rashin Tsaro Ya Fatattaki ‘Dan Takaran Shugaban kasa, Ya Hana Shi Taro a Katsina

  • ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar LP ya je Katsina domin ya yi kamfe a farkon makon nan
  • Peter Obi ya shirya zama da ‘yan gudun hijira, mata da matasan Katsina, amma hakan bai yiwu ba
  • Jam’iyyar ta samu labarin akwai barazanar tsaro, hakan ya jawo ‘Dan takaran ya fasa yin taron nan

Katsina – ‘Dan takaran LP, Peter Obi ya kai ziyara zuwa jihar Katsina a makon nan, ya yi niyyar zama da ‘yan gudun hijira amma hakan bai yiwu ba.

A wani rahoto na Sun, an samu labari cewa matsalar tsaro ta tilastawa ‘dan takaran shugaban kasar watsi da tattaunawar da ya yi niyyar yi da ‘yan IDP.

Peter Obi ya samu bayanai da ke nuna rashin tabbacin tsaro, a dalilin haka ya hakura da zaman.

Kara karanta wannan

Katon Kuskure ne Zaben Atiku Abubakar Inji Tsohon Hadiminsa da Ya Tona Masa Asiri

Da farko an tsara cewa Mista Obi zai zauna da ‘yan gudun hijira, mata, matasa da jagororin kungiyoyin dalibai na makarantun da ke jihar Katsina.

An shirya tsaf, dole aka hakura

An shirya za ayi zaman ne a dakin taro da biki na Munaj Event Centre da ke Katsina, amma a karshe barazanar tsaron bai bada damar yin hakan ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana fama da masu gudun hijira a jihar Katsina a sanadiyyar rashin tsaro da ya rutsa da wasu kauyuka, ‘yan bindiga sun kora mutane daga gidajensu.

Peter Obi
Mutanen Peter Obi a Gombe Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Daga baya ‘dan takaran kujerar shugaban kasar ya je filin wasa na Muhammadu Dikko, inda ya yi kira ga mutanen Katsina da su zabi jam’iyyar LP.

‘Dan takaran ya ce shi da abokin gaminsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed sun yi shirin gyara Najeriya.

Obi ya ce dole a bude iyakoki

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Gwamnan PDP a Arewa bai taba ganin sabbin Naira ba, ya tura sako ga Buhari

Jaridar ta rahoto tsohon Gwamnan na Anambra yana cewa idan suka kafa gwamnati, za a tsare rayuka da dukiyoyinsu, kuma a bude iyakoki.

"Ba za mu iya yakar talauci ba tare da samar da tsaro da kuma bude iyakoki ba. Zamu yaki talauci a kasar nan. Abin da muke shirin yi kenan a kan mulki.
Na san kun yi ta samun mulki a gwamnati, amma za ku yarda da ni mutanen nan yaudarar ku suke yi. Ina rokonku ku zabe mu, ku ga sabuwar Najeriya."

- Peter Obi

An kai wa tawagar Peter Obi hari

Labari ya zo cewa an kai wa tawagar Peter Obi hari a kan hanyarsu ta zuwa filin jirgi a Katsina, hakan ya faru da 'dan takaran har sau biyu a jihar.

A wata sanarwa da aka fitar, Kwamitin neman takara ya bukaci jami’an tsaro su binciki lamarin saboda gudun haka ta kuma faruwa nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel