An Haramtawa Wasu ‘Yan Najeriya Shiga Amurka, Atiku Ya Yi Maza Ya Yi Magana

An Haramtawa Wasu ‘Yan Najeriya Shiga Amurka, Atiku Ya Yi Maza Ya Yi Magana

  • Duk wanda yake yunkuri wajen kawo wani cikas a zabe mai zuwa zai gamu da fushin Amurka
  • Gwamnatin Joe Biden ta haramta mallakar takardar shiga kasar Amurka ga masu yin magudin zabe
  • Antony Blinken ya bada wannan sanarwa, ya ce haramcin za ta iya shafan iyalin wadannan mutane

Washington - Kasar Amurka ta dauki mataki a game da wasu ‘yan Najeriya da ake zargin su na neman kawowa tsarin damukaradiyya matsala.

Rahoton da aka fita daga The Cable a ranar Alhamis ya tabbatar da cewa Antony Blinken ya fitar da jawabi game da wannan batun a makon nan.

Sai dai Sakataren gwamnatin na kasar Amurka bai iya jero wadanda matakin ya shafa ba, amma ya ce ba za a ba su damar samun bizar kasar ba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gwamnan CBN ya ki zuwa majalisa kan batun sabbin Naira, kakaki ya fadi matakin da zai dauka

Antony Blinken yake cewa matakin da gwamnatinsu ta dauka zai iya yin tasiri a kan ‘yanuwa da iyalin mutanen da aka samu da laifin saba doka.

Amurka ta na daurewa damukaradiyya gindi

Babban jami’in kasar Amurkan yake cewa su na goyon bayan kafuwa da karfin damukaradiyya a Najeriya da sauran kasashen fadin Duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A dalilin tasgaron da wasu suke kawowa wajen tsarin mulkin farar hula a Najeriya, Punch ta rahoto Blinken yana cewa sun haramta masu yin biza.

Buhari
Muhammadu Buhari da Joe Biden Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnatin Biden tayi amfani da sashe na 212(a)(3)C) na dokar shige da fice da dokar zama ‘dan kasa wajen cin ma matsayar ana shirin zaben Najeriya.

A lokacin da zabe ya karaso, kasar Amurka za ta hukunta duk wani mai neman kawo matsala, shi ma zai shiga cikin sahun wadanda za a hana shi biza.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya rasu, wa zai maye gurbinsa? Ga abin da doka ta tanada

Rahoto ya ce gwamnatin kasar ketaren tayi karin haske cewa ba gwamnati ko wani ake hari ba, ana yaki da rashin gaskiya, a wanzar da bin doka ne.

Da yake magana a shafin Twitter da jin labarin, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna farin ciki.

‘Dan takaran kujerar shugabancin kasar yake cewa yana mai maraba da haramta samun biza ga irin wadannan mutane masu neman murde zabe.

Matsalar rashin fetur

An kafa kwamitin da zai magance matsalar wahalar fetur, an ji labari ‘yan kwamitin sun hada da shugaban kasa, Timipre Sylva da Zainab Ahmad.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Shugabannin hukumomin DSS, kwastam, EFCC da NSCDC sai shugabannin NMDPRA, NNPC, da gwamnan CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel