2023: Kada Ku Yarda Ku Mika Kasar Da Ke Fama Da Rashin Lafiya a Hannun Mara Lafiya, Peter Obi Ga Yan Najeriya

2023: Kada Ku Yarda Ku Mika Kasar Da Ke Fama Da Rashin Lafiya a Hannun Mara Lafiya, Peter Obi Ga Yan Najeriya

  • Peter Obi ya ce Najeriya bata da karfin da za a mika ta ga mutumin da bai da lafiya a babban zaben shugaban kasa mai zuwa
  • Dan takarar shugaban kasa na Labour Party ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a jami'ar Najeriya, Nsukka
  • Ya shawarci yan Najeriya da su yi hankali da wanda za su zaba a zabe mai zuwa saboda hakan na iya kara jefa kasar cikin hatsari

Enugu - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce kada yan Najeriya su kuskura su zabi mutumin da bai da lafiya a matsayin shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.

Obi ya bayyana hakan ne a jami'ar Najeriya da ke Nsukka, jihar Enugu a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Peter Obi
2023: Kada Ku Yarda Ku Mika Kasar Da Ke Fama Da Rashin Lafiya a Hannun Mara Lafiya, Peter Obi Ga Yan Najeriya Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Dan takrar na LP ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mara lafiya, cewa bai kamata a zabi mutumin da bai da lafiya a matsayin shugaban kasar ta ba a zaben shugaban kasa mai zuwa, Daily Trust ta rahoto.

Ya kuma ce bai kamata yan Najeriya su zabi kowani dan takarar shugaban kasa da ba zai iya tsayawa na tsawon mintina 30 ba, rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a san ainahin shekarun mutum ba amma yana son mulkar jama'a, Obi

Har wayau, Obi ya bukaci yan Najeriya da su duba halayya da aminci a babban zaben 2023 don gudun jefa kasar cikin karin matsala.

Wani bangare na jawabin Obi na cewa:

"Kasar nan bata da lafiya kuma bai kamata a mikata a hannun mara lafiya ba.
"Ba wai ina cewa wani bai da lafiya bane. Muna nan fiye da awa biyu, ba ma son mutane da ba za su iya tsayawa na mintuna 30 ba. A zaben kasar Amurka, su na zuwa muhawara, wani ya taba tambayar Barack Obama abubuwan da suka shafi rayuwarsa kuma ya amsa.

Kara karanta wannan

Ba lefe: Dan Arewa na cikiyar matr aure, zai ba ta sadaki N1m, amma ya fadi sharadi

"Amma a nan Najeriya, wani na son tsayawa takarar zabe, ba mu san ainahin shekarunsa ba, ba mu san sunansa ba, ba mu san makarantar da ya je ba. Babu wanda ya san ainahin wanene shi kuma yana son jagorantar kowa."

Kungiyar CAN ta ba matasa muhimmiyar shawara kan zaben 2023

A wani labarin, kungiyar CAN ta kiristocin Najeriya ta ja hankalin matasa kan muhimmancin zaben 2023, inda ta ce lallai kada su yarda su sai da kuri'unsu duk rintsi duk wuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel