Aure Shine Babbar Nasarata, Na Ga Tsiya Lokacin da Nake Layi, Inji Wata Mata

Aure Shine Babbar Nasarata, Na Ga Tsiya Lokacin da Nake Layi, Inji Wata Mata

  • Wata mata ta yada wani bidiyo don murnar yin aure, kuma ta ce shi ne babban nasaran da ta samu a rayuwarta
  • A cewar matar mai suna Ifunanya Ochei, ta tsiyar hali daga wurin mutane a lokacin da take gida ganin yadda ake mata magana
  • Ifunanya ta fadi a cikin bidiyon da ta yada a ranar 30 ga watan Disamba 2022 cewa, ta cika da fain cikin tun da ta yi aure

Wata mata ta yada wani bidiyo a shafinta na Instagram don bayyana jin dadi da farin ciki bayan da ta samu nasarar yin aure.

A bidiyon da ta yada a shafi mai hannun @unique.aiphy da suna Ifunanya Ochei ta ce rayuwar gwagware abin tausayi ne, kuma mai tsananin wahala.

Ifunanya ta ce ta ga tsiyar hali daga mutane kafin ta yi aure, saboda mutane kan yi amfani da wannan damar wajen fada maganganun banza.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Kama Hauka Tuburan a Abuja, Ta Nemi Wata Angela Ta Rabu da Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

Matar aure ta bayyana dadin da ta ji bayan yin aure
Aure Shine Babbar Nasarata, Na Ga Tsiya Lokacin da Nake Layi, Inji Wata Mata | Hoto: /@unique.aiphy
Asali: Instagram

Ta samu shiga, ta yi wuff da wani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yanzu dai ta samu shiga gidan mijinta, ta ce a yanzu ta shiga farin ciki cikakke kamar yadda take buri.

A cewar Ifunanya, a yanzu sunanta matar aure kuma uwar gida kuma ta kan ji dadi da farin ciki ya lullube ta duk sadda ta farko ta ganta a gidan miji ga kuma mijin a tare da ita.

Ta ce:

"Shekra daya bayan aure, gaskiyar cewa wai na yi aure na ci gaba da kada ni."

Bidiyon da ta yada a ranar 30 ga watan Disamban bara ya dauki hankali, kuma mutane da yawa ne suka yi martani a kansa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa a karkashin bidiyon da matar ta yada:

@ugokingsdonkil:

"Lols! Ify kina da ban dariya! Tsawon lokaci 'yar uwa. Na yi kewarki da yawa."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dumu-dumu Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Masa Sata, Tayi Borin Kunya Kiri-kiri

@chelinstreats:

"'Yar uwa ba abu ne mai sauki yin aure ba. Wani lokaci wasu sun ce ke kike da zabi."

@loistruly:

"Gaskiya ne. Mata mai karfi ko kuma in ce matar da a zahiri bata tsoron abin da mutane za su yi tunanin me za ta yi ba kuma take abin da ke gabanta. Ko kin yi ko baki yi za su yi magana, to kawai ki yi."

Budurwa ta nuna tana son saurayi

A wani labarin kuma, wata budurwa ta tsokani wani mutumin da ke tsaye, ta ce ya biyo ta su tafi, tana kaunarsa.

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana ko dai mutumin yana cikin wani yana yi ne.

A bangare guda, mutumin ya nuna ba ya yinta, don haka ya bayyana mata kara cewa ba zai bi ta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel