'Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara, Sun Gano Mutum Biyu Da Ake Zargi

'Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara, Sun Gano Mutum Biyu Da Ake Zargi

  • Hukumar 'yan sanda ta jihar Zamfara ta ce jami'anta sun yi ram da muggan makamai a hannun wasu mutum biyu
  • Mai magana da yawun hukumar, Muhammad Shehu, ya ce wadan da ake zargin sun amsa laifin kaiwa yan bindigan Jeji makamai
  • Kwamishinan yan sanda, Kolo Yusuf, yace rundunarsa zata ci gaba da yaki don kare rayuwa da dukiyoyin al'umma

Zamfara - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Zamafara ta sanar da cewa dakarunta sun cafke wasu mutane biyu dauke da Alburusai 325 a kan Titin Gusau-Wanke-Dansadau.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Jami'an yan sanda.
'Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara, Sun Gano Mutum Biyu Da Ake Zargi Hoto: vanguard
Asali: UGC

Ya ce waɗan da ake zargin sun shiga hannun dakarun 'yan sanda ne ranar 8 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 11:00 na dare.

Kara karanta wannan

'Yan Sandan Anambra Sun Kama Matashi Kan Fada, Ya Mutu a Hannunsu

Shehu ya kara da cewa wadan da ake zargin, Emmanuel Emmanuel da wata mace mai suna, Nana Ibrahim, an kama su dauke da Alburusai 325 da bindigar AK-47 guda ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yace sun samu wannan nasara ne bayan samun wasu sahihan bayanan sirri game da safarar makamai daga jahar Benuwai zuwa sansanin 'yan fashin jeji a Zamfara.

A cewarsa, asirin wadanda ake zargi ya tonu ne yayin da Jami'an sashin dabaru ke gudanar da bincikem ababen hawa a kan Titin.

Muhammad Shehu yace tuni aka fara bincikar mutanen, kuma sun yi bayanin cewa suna da hannu a kasuwancin safarar makamai ga yan bindiga a Zamfara da wasu makotan jihohi.

Wane mataki hukumar ta dauka kan lamarin?

Kakakin yan sandan yace, "Za'a ci gaba da bincike kan mutanen biyu domin a kamo sauran masu agaza masu daga bisani a gurfanar da su gaban Kotu."

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar, FG

Shehu ya ce Kwamishinan 'yan sandan jihar, Kolo Yusuf, ya tabbatar da cewa rundunarsa zata ci gaba da kokaren kare al'umma kana ya nemi hadin kan jama'a, The Nation ta ruwaito.

A wani labarin kuma An Kama Daya Daga Cikin Miyagun Da Suka Yi Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa A Najeriya

Gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa gamayyar jami'an tsaro sun kama mutum daya da ake zargi da hannu a garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a jihar.

A cewar gwwamnan, wanda ake zargin yabfara bayani kuma yana taimaka wa jami'ai domin ceto mutanen da yan ta'addan suka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel