Gwamnatin Tarayya Ta Lissafo Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar

Gwamnatin Tarayya Ta Lissafo Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar

 • Daga karshe, gwamnatin tarayya ta fara shirin nada sabon Akanta Janar na tarayya AGF
 • Bayan tantancewa da sahalewar hukumomin yaki da rashawa, an fitar da sunayen mutum 20
 • Za'a zanna da wadannan mutane kuma a sake tantacesu sannan a zabi daya cikinsu

Gwamnatin tarayya ta lisaffo jerin sunayen mutum ashirin da cikinsu ake kyautata zaton zaben sabon Akanta Janar na tarayya watau AGF.

TheCable ta ruwaito cewa an fitar da sunayen mutum 20 masu aiki yanzu haka a wasu ma'aikatu daban-daban.

A Mayu, mun kawo muku yadda aka damke tsohon Akanta Janar Ahmed Idris a jihar Kano bayan zargin handamar makudan biliyoyi da hukumar hana ta'annati da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ke masa.

EFCC ta ce da hannun Ahmed Idris an handami kudi N109bn.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu Yana Taba Kirifto Ne: Yasha Alwashin Taimakon Yan Kirifto In Ya Kai Ga Gaci

Bayan cireshi, Ministar Kudi ta nada Chukwunyere Anamekwe matsayin mukaddashin Akanta Janar amma kuma shima aka sameshi da kashi a gindi kuma aka cireshi.

Ahmed idris
Gwamnatin Tarayya Ta Lissafo Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda suka nemi kujerar

Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadanda suka nemi kujerar Akanta Janar bayan hukumomin yaki da rashawa sun gudanar da bincike kansu.

Takardar yace ranar Litnin, 9 ga Junairu za'a fara tantancesu.

A cewar takardar:

"Saboda haka, ana kira ga wadannan yan takara su garzayo zaman tantancewa da aka shirya yi daga ranar Litinin 9 zuwa Laraba 11 ga Junairu, 2023 a Olusegun Obasanjo Hall, ofishin shugabar ma'aikatan gwamnati Federal Secretariat, Phase lI, Abuja tsakanin karfe 8 na safe zuwa karfe 4."

Ga jerin sunayen wadanda aka zabe:

 1. Mufutau Bukola (Transportation),
 2. Mohammed Aminu Yara’abba (Federal Fire Service),
 3. Danladi Zakowi Comfort (Interior),
 4. Mahmud Adam Kambari (North East Dev. Comm)
 5. Mohammed Magaji. M. Doho (Interior)
 6. Waziri Amos Samuel (Agric and Rural Development)
 7. Madein Oluwatoyin Sakirat (OHCSF)
 8. Adaramoye Joseph Oluwole (Humanitarian Affairs)
 9. Isa Abubakar (Science, Tech & Innovation)
 10. Ogunsemowo Oladipupo Olakunle (Environment)
 11. Egbokale Kadiri Charity (Nig. Football Federation)
 12. lbrahim Saadiyya Jibo (National Boundary Commission)
 13. Ogbodo Chinasa Nnam (National Salaries, Income & Wages Commission)
 14. Bakre Modupe Julianah (NPF)
 15. Osakwe Udechukwu Obi (Health)
 16. Velvuk Abubakar Sadiq (OAGF)
 17. Njeze Bertrand Chukwuma (Surveyors Council of Nigeria)
 18. Wali Charled Metule (Special Duties & Intergovernmental Affairs)
 19. Dandela Abdulrahman Kassim (Police Affairs)
 20. Mohammed Munkaila (Works & Housing).

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel