Yaron da 'Yan Sanda Suka Kama Kan Fada, Ya Sheka Lahira a Caji Ofis

Yaron da 'Yan Sanda Suka Kama Kan Fada, Ya Sheka Lahira a Caji Ofis

  • Ana zargin jami'an 'yan sandan yankin Akwuzu da ke jihar Anambra da halaka wani yaro da aka kama kan laifin fada da wani
  • Bayan 'yan sandan sun bukaci belin Uchenna kan N150,000, iyayensa sun je wurin amma aka sanar musu yace ga garin ku
  • Sai dai rundunar 'yan sanda ta musanta faruwar lamarin inda suka ce an kama Uchenna ne kan zargin fashi da makami

Anambra - Ana zargin rundunar 'yan sandan jihar Anambra da ke da caji ofis a Akwuzu da kama wani yaro mai suna Uchenna Okafor inda ya sheka lahira a hannunsu.

Wani mai rajin kare hakkin 'dan Adam ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter.

Taswirar Anambra
Yaron da 'Yan Sanda Suka Kama Kan Fada, Ya Sheka Lahira a Caji Ofis. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Ma'abocin amfani da Twitter din yace an kama yara maza uku a makon da ya gabata kan fada kuma an sanar da iyayensu abinda ke faruwa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar, FG

Kamar yadda ma'abocin amfani da Twitter din yace, an bukaci iyayen Uchenna da su kawo N150,000 don a saki 'dan su amma yayin da suka isa caji ofis din a ranar Alhamis, an sanar musu cewa 'dansu yace ga garin ku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, CDP Olumuyiwa Adejobi, yayin martani ga wallafar, yace:

"Na bukaci kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra da ya duba wannan lamarin kuma yayi martani."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, yayin martani ta wata takarda a ranar Litinin yace:

"Yayin da muke cigaba da duba zargin, bayanan da suke gabanmu na nuna cewa ba fada suka yi ba, amma zargin fashi da makami ne ke gabanmu.
"Muna tsammanin ma'aboci amfani da Twitter din zai zo ofishin hukumar da safen nan da karin bayani. Hakazalika, IPO din da ke rike da kes din ana tsammanin zai kawo bayani da safen nan. Mun gode."

Kara karanta wannan

Borno: Sojin Najeriya Sun yi Nasarar Halaka 'Yan Boko Haram 4, Sun Tarwatsa Sansanoninsu 6 Sabbi a Mafa

Bidiyon budurwa tana kuka bayan ta debo ciki a waje

A wani bidiyo na daban, wata budurwa ta fara sabuwar shekararta da tashin hankali maras misaltuwa bayan ta debo ciki a waje kuma babu aure.

Budurwa cike da hawaye ta sanar da cewa bata san yadda za ta fara sanar da mahaifiyarta ba bayan da tayi gwajin da ke nuna tabbas tana da ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel