2023: Matar Obi Ta Yiwa Mata Alkawarin Samun Kudi a Gwamnatin Mijinta

2023: Matar Obi Ta Yiwa Mata Alkawarin Samun Kudi a Gwamnatin Mijinta

  • An ba matan Najeriya tabbacin cewa ba za a wofantar da rawar ganin da suke takawa wajen gina sabuwar Najeriya
  • Matar dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Margaret Obi yi alkawarin cewa gwamnatin mijinta zai ba mata damar samun kudi
  • Ta kuma bayyana cewa mata za su samu damar koyon sana’o’i da shiga ayi da su a gwamnati

Abuja - Margaret Obi, uwargidar dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi ta yi wasu muhimman alkawara ga matan Najeriya gabannin zaben shugaban kasa na 2023.

Da take jawabi a wani taron mata a Abuja, matar tsohon gwamnan na jihar Anambra ta nuna takaici yadda ake barin mata a baya duk da sune kaso 49 na al'ummar kasar, Thisday ta rahoto

Margaret Obi
2023: Matar Obi Ta Yiwa Mata Alkawarin Samun Kudi a Gwamnatin Mijinta Hoto: Margaret Obi
Asali: Facebook

Margaret ta bayyana cewa gwamnatin Peter Obi za ta kawo sauyi ga mata wanda suka hada da samun kudade, kiwon lafiya mai inganci, tallafi na tattalin arziki da kuma shiga ayi da su a gwamnati.

Kara karanta wannan

Dirama, Wani Dan Kasuwa Ya Hargitse a Kotun Musulunci Kaduna, Yace Yana Kaunar Matarsa

Ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Me zai sa mu dunga shan wahala ta karkashin kasa? Wannan ne dalilin da yasa muke wannan kiran ga mata, za ku iya kuma dole ku tallafawa kasar don haihuwar sabuwar Najeriya. Lokacin da abubuwa suka tabarbare, mata ne suka fi shan wahala. Saboda haka ina karfafa maku gwiwa da ku dubi abun da yan takarar za su yiwa mata. Ku dubi tarihin da suka kafa sannan ku zabi wanda ya dace.
“Daga samun kudi zuwa cibiyar lafiya da tallafi na tattalin arziki da kuma damawa da su a gwamnati.”

Margaret ta kuma bayyana cewa gwamnatin mijinta ta tanadi tsare-tsare na musamman don tallafawa mata, rahoton punch.

Ta kara da cewar:

"Wannan ne dalilin da yasa ya zama dole ku fito ku zabi ObiDatti da zabar Labour Party."

Obi ya samu goyon bayan Edwin Clark

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Dage Sai Ya Cire Tallafin Fetur Idan Ya Gaji Buhari

A wani labarin, mun ji cewa wani babban jigon kasa kuma jagoran al'ummar Ijaw na Neja Delta, Cif Edwin Clark, ya nuna cikakken goyon bayansa ga takarar Peter Obi.

Dattijon ya bayyana cewa Obi ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya a babban zaben 2023 mai zuwa.

A cewarsa, tsohon gwamnan na jihar Anambra na da halin shugabanci nagari irin wanda Najeriya ke bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel