2023: Kasa Da Awanni 72 Bayan Obasanjo Ya Lamunce Masa, Edwin Clark Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Obi

2023: Kasa Da Awanni 72 Bayan Obasanjo Ya Lamunce Masa, Edwin Clark Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Obi

  • Sansanin jam'iyyar Labour Party na kara samun karfi gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023
  • Dan takarar shugaban kasa ka na jam'iyyar LP, Peter Obi ya samu gagarumin goyon baya a zaben shugaban kasa na wata mai zuwa
  • Jigon kasa kuma shugaban kungiyar al'ummar Ijaw a Neja Delta, Cif Edwin Clark ya ayyana goyon bayansa ga tsohon gwamnan na jihar Anambra

Abuja - Kasa da awanni 72 bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi, dan takarar na jam'iyyar Labour Party, ya sake samun goyon baya daga jigon kasa, Cif Edwin Clark.

A cewar Channels TV, Cif Clark ya ayyana goyon bayansa ga Obi a Abuja, babban birnin tarayyar kasar a wani taron manema labarai a ranar Talata, 3 ga watan Janairu.

Clark da Obi
2023: Kasa Da Awanni 72 Bayan Obasanjo Ya Lamunce Masa Edwin Clark Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Obi Hoto: Chief Edwin Clark, Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Obi na da halin shugaba nagari

Ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra na da hali na shugabanci kuma cewa shine dan takarar da Najeriya ke bukata don gyarawa da fitar da ita daga halin da take ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban jigon kaar ya bayyana cewa Obi na da halin shugaba nagari, wanda ya nuna a yayin da yake jagorantar mutanen jihar Anambra a matsayin gwamna tsawon shekaru takwasa.

Sai dai kuma, ya bukaci dan takarar shugaban kasar na Labour Party da ya kawo karshen rashin adalcin da ake yiwa mutanen Neja Delta da kawo karshen gurbatar muhalli a yankin.

A cewar jaridar Vanguard, an nakalto jigon kasar na cewa:

"Ana marhaba da jajircewar Peter Obi na tsaftace gurbatattun garuruwa a Neja Delta, duba ga cewar shirin tsafta na Ogoni na tafiyar asha ruwan tsuntsaye."

"Jajircewarsa na aiki da kwararrun yan Neja Delta a tsarin mulkin kasa a gwamnati mai zuwa idan aka zabe shi a kan karagar mulki abu ne mai tabbatuwa.”

Cif Edwin Clark shine babban jigon kasa na biyu da ya lamucewa dan takarar shugaban kasar na Labour Party.

A wani labarin, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, ya goyi bayan mara wa Peter Obi baya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi.

A wani sako da ya saki na sabon shekara, Obasanjo ya mara wa takarar shugabancin Obi baya, yana mai cewa dan takarar na LP ya fi sauran yan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel