Wani Dan Kasuwa Ya Rikice a Kotun Musulunci, Yace Yana Kaunar Matarsa Bai Sake Ta Ba

Wani Dan Kasuwa Ya Rikice a Kotun Musulunci, Yace Yana Kaunar Matarsa Bai Sake Ta Ba

  • Wani magidanci dan kasuwa ya shaida wa Kotun shari'ar Musulunci mai zama Magajin Gari Kaduna cewa bai saki matarsa ba
  • Da yake martani kan karar da Bashirat ta shigar da shi, Abubakar yace yana kaunar matarsa haka nan ta tattara ta bar gida
  • Mallam Rilwanu Kyaudai, Alkalin Kotun ya nemi mai kara ta kawo hujja kana ya dage zaman ko zasu iya sulhu a tsakaninsu

Kaduna - Wani dan kasuwa mai suna Hassan Abubakar, ranar Talata ya musanta cewa ya saki matarsa, Bashirat Abdulrazak, a Kotun shari'a mai zama a Magajin Gari, Kaduna.

Abubakar ya shaida wa Kotu cewa yana kaunar matarsa kuma ba shi da niyyar rabuwa da ita, kamar yadda rahoton jaridar Daily Nigerian ya tabbatar.

Kotun Shari'a a Kaduna.
Wani Dan Kasuwa Ya Rikice a Kotun Musulunci, Yace Yana Kaunar Matarsa Bai Sake Ta Ba Hoto: dailynigerian
Asali: Facebook

Magidancin ya ce:

"Mun haifi ɗa guda ɗaya tare, wata rana na dawo gida kenan daga wurin kasuwanci na sai na taras ta kwashe dukkanin kayanta daga gida. Babu sabani a tsakanin mu ko rashin fahimta."

Kara karanta wannan

Kan Abu Daya, Kotun Musulunci a Kaduna Ta Raba Ango Da Amarya Watanni Uku da Daura Masu Aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun fari dai, mai shigar da kara, Bashirat Abdulrazak ta fada wa Alkalin Kotun cewa Mijinta ya ambata mata kalmar saki da bakinsa.

A cewarta, bisa haka ne ta garzayo Kotu tana rokon Alkali ya tabbatar da wannan sakin da mai gidanta ya yi mata.

Bashirat ta ce:

"Kuma ina son a umarce shi ya dauki dukkan nauyin dan da muka haifa kuma ya fadi yadda zai iya biya a matsayin kudin ciyar da ɗansa."

Wane mataki Kotun ta dauka?

Alkalin Kotun shari'a ta Magajin Gari Kaduna, Mai shari'a Mallam Rilwanu Kyaudai, ya bukaci wacce ta shigar da kara ta kawo shaidun da zasu tabbatar da zargin da take cewa Mijin ya sake ta.

Daga nan ya dage zaman zuwa ranar 19 ga watan Janairu, 2023 domin ba ma'auratan dama su bi hanyar sulhunta junansu ko kuma matar ta kawo shaidu idan kokarin sulhun ya ci tura.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Fitaccen Sarki a Arewa, Sun Tafka Ta'asa

A wani labarin kuma Kyakkyawar Budurwa Ta Kashe Aurenta Na Watanni 3, Ta Saki Hotunan Bikinta

Wata matashiyar ‘yar Najeriya mai suna Bolaghold ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa aurenta na watanni uku ya mutu murus.

Matashiyar ta bayyana cewa babu ta yadɗa matsaloli zasu zama masalaha kuma ba dole sai mace da namiji sun yi aure sannan Allah zai basu haihuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel