Tsarin Babban Bankin Kasa Akan Fitar Da Kudi Kaman Takewa ‘Yan Nijeriya Hakk'i Ne

Tsarin Babban Bankin Kasa Akan Fitar Da Kudi Kaman Takewa ‘Yan Nijeriya Hakk'i Ne

  • Babban bankin Nigeria CBN ya yace ya sauya kudin kasar ne domin magance tare da inganta tattalin arzikin kasar
  • A ranar 15 ga wanta Nuwanba Bankin ya kaddamar da sabin kudaden a fadar shugaban kasa, kuma yace tsoffin zasu daina aiki a 31 ga watan Junairun 2023
  • Kiminanin Naira Tiriliyan 2.3 ne ke yawo a hannun mutane a Nigeria, kamar yadda rahotan babban bankin ya nuna kafin sake kud'ad'en fasali

Abuja: Masanin harkokin kudi Dakta Muda Yusuf, ya bayyana tsarin da babban bankin kasa ya fito dashi na kayyade cire kudi a matsayin tauye hakkin ‘yan Najeriya musamman ma marasa amfani da banki.

A cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar Talata, ya sanar da kayyade adadin kudaden da mutane da kungiyoyi zasu na cirewa daga ranar 9 ga watan Janairu 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Hadu da Shugaban Kasa, Ya Yi Maganar Janye Dokar Kayyade Kudi

Bankin ya ba da umarnin fitar da tsabar kudi ga d'aid'aikun mutane da kamfanoni kan N100, 000 da N500, 000 a kowane mako. Har ila yau, ya ba da umarnin a rika sa 'yan 200 zuwa kasa a ATM.

A zaman majalissa da akayi jiya ranar Laraba, wasu Sanatoci sun nuna damuwa game da sabuwar manufar tare da fargabar cewa za a yi wa yawancin ‘yan Najeriya mummunar illa.

Dr Moda
Tsarin Babban Bankin Kasa Akan Fitar Da Kudi Kaman Takewa ‘Yan Nijeriya Hakk'i Ne Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yau Alhamis, majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan sabon tsarin da bankin ya fito da shi.

Ga Abinda Wani Masani yace Game Da Batun

Sai dai Dr Muda Yusuf a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya bayyana ikirarin da CBN d'in ya yi cewa akwai kudi da yawa a hannun mutane a matsayin kuskure.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Ya kara da cewa:

"Sabon tsarin zai yi mummunan tasiri a b'angaren tattalin arzikin da ba na yau da kullun ba, inda ya kara da cewa bangaren da ba na yau da kullun ba shi ne muhimmin bangare na tattalin arzikin da ke da samar da kashi 80% na tattalin arzikin Najeriya da kuma wasu muhimman ayyukan yi Najeriya. .

Dokta Yusuf ya yi nuni da cewa, akwai bukatar bankin CBN ya yi tunani da wannan manufa yadda ya kamata domin kaucewa haifar da matsaloli fiye da yadda ya tsara a magance.

:"Kud'ad'en da ke zagayawa a hannun mutane a karshen watan Oktoban wannan shekarar ya kai naira tiriliyan 3.2, wanda kuma a zahirinsu wanda mutane ke rikewa da hannunsu ya kai naira tiriliyan 2.3".

Dakta Yusuf ya kara da cewa:

"Akwai bambanci tsakanin samar da kudi da kuma abinda kudin zai kawo, jimillar kudin da aka samar a watan Oktoban 2022 ya kai Naira tiriliyan 50.6. Jimillar kudaden da ake samu a tattalin arzikin kasar nan Naira tiriliyan 3.3 ne kawai, wanda kashi 6.5 ne kawai na kudin da ake samarwa. Wanda jimillar kuɗaɗen sun tasarma kashi 5.5."

Kara karanta wannan

Fata-fata Kenan: Jama'a Sun Dauki Dumi Bayan Ganin Wani Kalan Takalmi Da Peter Obi Ya Sanya A Wurin Taro

Har ila yau, akwai hadarin cewa wannan tsarin zai dakatar da hada-hadar kudi kamar yadda CBN ke tunani. Wasu daga cikin ma’aikatan da ba na yau da kullun ba na iya gujewa tsarin banki gaba daya.

Dr Yusuf ya 'kar'kare da cewa,

"Haka zalika hakan na iya zama cin zarafi ga 'yan Najeriya da ba su da banki, akwai bukatar bankin CBN ya yi tunani kan wannan tsarin yadda ya kamata domin kaucewa haifar da matsaloli fiye da yadda ta tsara magancewa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel