Badakalar Kudi Ta Sa EFCC Ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kaduna da Wasu Mutane

Badakalar Kudi Ta Sa EFCC Ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kaduna da Wasu Mutane

  • An sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna bisa zargin badalakar kudade masu nasaba da tsohuwar minista
  • An kuma gurfanar da wasu tsoffin jiga-jigai a kasar tare da gwamnan bisa zargin hannu a badakalar kudin
  • A baya an gurfanar dasu a kotun tarayya mai zamanta a Kaduna, amma aka samu akasi, yanzu an fara sabuwar shari'a

Jihar Kaduna - Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Yero kan batutuwan da suka shafi badakalar kudi.

An sake gurfanar da Yero ne tare da wasu abokan harkallarsa a babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kaduna kan wasu laifuka takwas da EFCC ta gabatar, Premium Times ta ruwaito.

A cewar kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, laifukan da ake tuhumar Yero suna da alaka da kudaden da suka kai N700m masu nasaba da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke gabanin zaben 2015.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Bada Umarni a Karbe Miliyoyi da Gidajen Hadiman Sambo Dasuki Har Abada

EFCC ta yi zargin cewa, an sake kudaden domin karkatar da da sakamakon zaben 2015 domin ganin nasarar PDP a zaben.

Kotu ta sake gurfanar da Ramalan Yero na jihar Kaduna
Badakalar Kudi Ta Sa EFCC Ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kaduna da Wasu Mutane | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka gurnar da Yero dasu sun hada da Nuhu Samo Wya (tsohon minsita), Ishaq Hamza (tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna) da Abubakar Gaiya Haruna (tsohon shugaban PDP a Kaduna).

Yadda shari'ar ta kasance a baya

A tun farko an gurfanar dasu a gaban mai shari'a M.G Umar a babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna.

An sake gurfanar dasu a gaban mai shari'a, R.M Aikawa bayan da aka yiwa M.G Umar sauyin wurin aiki, Vanguard ta ruwaito.

An sake sabuwar shari'a ne daga farko a gaban Aikawa a ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba.

Yero da sauran wadanda ake zargin sun muzanta zargin da ake musu yayin da aka karanto musu laifukansu.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai

Bayan haka ne, lauyan wadanda ake kara, Yunus Ustaz Usman ya bukaci kotu da ta duba lamarin wadanda ake kara tare da ba da belinsu kamar yadda alkali a bayar ya bayar.

A bangarensa, lauyan mai shigar da kara Nasiru Salele da ya bayyana tare da M.E Eimonye da P.C Onyenebo bai kalubalanci bukatar belin ba.

Mai shari'a Aikawa ya ba da belin wadanda ake zargi kamar yadda aka bayar a baya, kana ya dage sake sauraran shari'ar zuwa 16, 17 da 18 na watan Janairun 2023.

Duk da abin da yake fuskanta, yero ya bayyana sake tsayawa takarar gwamna a jihar ta Kaduna, lamarin da bai kai ga gaci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel