Bana Tsoron Komai, Alhaji Tukur Mamu da Aka Kama a Kasar Masar Ya Magantu

Bana Tsoron Komai, Alhaji Tukur Mamu da Aka Kama a Kasar Masar Ya Magantu

  • Matawallafin jarida, Tukur Mamu ya magantu da jaridar Najeriya bayan da aka kama shi a kasar Masar
  • Ya ce ba a kama shi da kayan aikata laifi ba, don haka bai jin tsoron komai da zai iya faruwa dashi
  • Hukumomin kasar Masar sun shirya dawo da Mamu Najeriya bisa umarnin gwamnatin Najeriya

Alkahira, Masar - Fitaccen dan jarida kuma wallafin kafar labarai a Arewacin Najeriya, Alhaji Tukur Mamu dake zaune a Kaduna ya magantu bayan da jami'an tsaro suka kwamushe shi a kasar Masar.

A yau Laraba 7 ga watan Satumba ne aka tashi da labarin kame Mamu a birnin Alkahira na kasar Masar bisa umarin gwamnatin Najeriya.

Mamu dai na daya daga cikin mutanen dake tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace mutane da yawa a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Tinubu da Atiku Sun Yi Wa Mata Alkawarin Fiye da Abin da Suke Nema a Gwamnati

Tukur Mamu ya magantu bayan kama shi a Masar
Bana tsoron komai, Alhaji Tukur Mamu da aka kama a kasar Masar ya magantu | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A bayanan da ya bayar, Mamu ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa Umrah ne kasa mai tsarki, inda aka kama shi a filin jirgin Alkahira, kuma za a dawo dashi Najeriya cikin sa'o'i 24.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babu wani abu da aka kama ni dashi, inji Mamu

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust a lokacin da yake cikin jirgin da za a dawo dashi Najeriya, Mamu ya ce ba a same shi da wani abu na aikata laifi tare dashi ba.

Ya kara da cewa hukumomin kasar Masar sun bayyana masa cewa ba su da wata hujjar ci gaba da tsare shi.

Ya shaidawa Daily Trust cewa:

"Akan hanyata ta zuwa Alkahira - Masar nake amma inda na nufa Saudiyya ne domin na yi Umrah tare da wasu ‘yan uwana.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

“An ajiye ni tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin saman Alkahira bisa umarnin gwamnatin Najeriya.
“Ba a ci zarafi na a filin jirgin saman Najeriya ba har sai da na isa birnin Alkahira inda jami’an tsaro dake wurin suka ce min hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta ba da umarnin a kama ni.
"An tsare ni ne tare da ahali na tsawon yini guda a filin jirgin saman Alkahira."
“Yanzu haka sun kama jirgi na gaba domin a taho da ni da ahalina zuwa gida Kano. Na tabbata jami’an DSS za su jira saukarmu a filin jirgin saman Kano a yau (Laraba).
"Babu wani abu da nake boyewa kuma ba na jin tsoronsu (DSS) na rantse da Allah ba na tsoronsu, ina dai son duniya ta san abin da ke faruwa ne kawai."

Gwamnatin Najeriya ta sha zargin Mamu da bin tsagin 'yan ta'adda maimakon kare muradin gwamnati, batun da yake yawan musantawa.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

An Damke Tukur Mamu A Kasar Misra Bisa Umurnin Gwamnatin Tarayya

A wani labarin, jami'an tsaron birnin Kahira a kasar Masar sun damke mai kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da iyalansa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Tukur Mamu na hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya gudanar da Ibadar Umrah yayinda aka tsareshi a tashar jirgin Kahira na kwana guda.

Rahoton yan kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta bukaci a damkeshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel