Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Dakin Kwanan Dalibai a Makarantar Tsangaya a Jihar Kano

Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Dakin Kwanan Dalibai a Makarantar Tsangaya a Jihar Kano

  • Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wata makarantar Tsangaya a jihar Kano, kamar yadda hukumar agaji ta tabbatar
  • Akalla dakuna 14 ne suka kone kurmus, NEMA ta ba da tallafi mai yawa ga daliban makarantar
  • Gwamnati ta shawarci jama'a kan mu'amalantar wuta da kayayyakin da suke da alaka da gobara a jihar Kano

Madobi, jihar Kano - Wata mummunar gobara ta yi kaca-kaca da dakuna 14 na wata makaranta mai suna Tsagya Model Boarding Primary School a yankin Kanwa ta karamar hukumar Madobi a jihar Kano.

Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA), Dr Saleh Jili ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya kawo kayan rage radadi ga makarantar, Daily Trust ta ruwaito.

Makarantar Tsangaya ta kone kurmus a jihar Kano
Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Dakin Kwanan Dalibai a Makarantar Tsangaya a Jihar Kano | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce:

"Mun zo ne a madadin gwamna Abdullahi Ganduje domin jajantawa makatantar da kuma ba da tallafin rage radadi tare da fatan hakan zai rage radadin garesu."

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayayyakin gudunmawar da aka bayar

Jili ya bayyana cewa, daga kayayyakin da gwamnati ta bayar akwai buhunna 20 na masara, 20 na shinkafa, 2 na Maggi, man gyada, bargo 212 da kuma gidan saura 212.

Sauran kayayyakin sun hada da tabarmai, bokitin roba, farantin cin abinci, kofuna da cokula, rahoton Global Patriot News ta ruwaito.

Ya bukaci jama'ar gari, musamman mata masu amfani da murhun itace, gas da gawayi su kula kuma ake kashe kayayyakin wutar lantarki duk lokacin da ba a amfani dasu.

A nasa bangaren, shugaban hukumar makarantun Islamiyya da Tsangaya a jihar Kano, Gwani Yahuza Danzarga ya yaba wa gwamna Ganduje da hukumar NEMA bisa wannan halin kirki.

Ya ce:

"Mun godewa Allah madaukakin sarki cewa cikin 211 na daliban na makarantar babu wanda ya samu rauni.
"Lamarin ya daru ne a lokacin da daliban ke karatun yamma. Dukkan dakuna 14 na wurin kwanan ya kone kurmus."

Kara karanta wannan

Akwai rikici a kasa: DSS ta gano sirrin 'yan siyasa, za su yi amfani da 'yan daba a 2023

Mai garin Kanwa, Alhaji Isyaku Maitama, wanda ya samu wakilcin Umar Maitama ya yabawa hukumar NEMA kan wannan tallafi da suka kawo.

Mazaunin yankin ya fadi yadda lamarin ya faru

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, Malam Rilwani Kanwa, wanda ya tabbatar da yadda gwamnati ta kawo dauki ga daliban makarantar.

Ya kuma bayyana cewa, tuni dalibai sun koma karatu, ko yau dinnan Litinin 7 ga watan Nuwamba, dalibai sun yi karatu.

A cewarsa:

"Bamu san musabbabin tashin gobarar ba, kasancewar babu wutar lantarki a makarantar kuma yara ne ba girki suke ba, sai dai mu ce kaddara ne.
"Dalibai sun koma makaranta, kuma sun samu tallafi daga gwamna, shugaban karamar hukuma, matarsa da sauran manyan yankin.
"An ba su sutura, an ba su kayan abinci, an ba su bargo da dai sauransu."

Akwai Yuwuwar ’Yan Siyasa Su Yi Amfani Da ’Yan Daba Wajen Gangamin Kamfen Zaben 2023, Inji DSS

Kara karanta wannan

Madalla: Buhari ya tuna da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, ya ba su wani babban tallafi

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadin cewa, akwai yiwuwar 'yan siyasa a kasar nan su yi amfani da tsagerun 'yan daba a gangamin su na zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan DSS a Kaduna, Mr Abdul Enachie yayin gabatar da rahotonsa kan tsaro a jihar ta Kaduna.

Ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnati ta mai da hankali sosai tare da wayar da kan matasa don gudun amfani dasu wajen aikata barna a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel