Babu Shugaban Kasa Irin Buhari A Tarihin Najeriya – Kakakin APC

Babu Shugaban Kasa Irin Buhari A Tarihin Najeriya – Kakakin APC

  • Alhaji Yusuf Idris ya yabawa Shugaba Buhari kan yadda ya inganta rayuwar talakawa a fadin kasar
  • Kakakin APC a Zamfara ya ce Buhari kasai ne ya aiwatar da shirin zuba jari a tarihin shugabancin Najeriya
  • Idris ya ce hatta ga masu sukar gwamnatin Buhari sun amfana daga wadannan shirye-shirye

Abuja - Sakataren labarai na jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Yusuf Idris, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abubuwan da ya cancanci a yaba masa a kasar nan.

A cewar kakakin na APC, ba a taba shugaban kasa irin Muhammadu Buhari a tarihin Najeriya, Jaridar Vanguard ta rahoto.

Shugaban Buhari
Babu Shugaban Kasa Irin Buhari A Tarihin Najeriya – Kakakin APC Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Idris ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja cewa shugaban kasar yayi namijin kokari a shekaru bakwai da suka gabata.

Kara karanta wannan

Barazanar Harin Abuja: Daga Karshe, Buhari Ya Yi Martani, Ya Ce "Ana Samun Nasarar Shawo Kan Rashin Tsaro"

"Sai dai, ya zama dole a kara wayarwa jama'a da kai kan tsare-tsare da manufofI da kuma nasarorin gwamnatin Buhari."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya bayyana cewa a tarihin shugabancin Najeriya, Buhari ne kadai ya kaddamar da shirin zuba jari da ke da manufofi iri-iri.

Ya kara da cewa wadannan manufofi sun amfani talakawa da dama a fadin kasar nan.

Ya jero wadannan shirye-shirye da suka hada da na N-Power, tallafin kudi, TraderMoni da shirin tallafawa tsoffi da sauransu.

“Idan kuka duba zaku gano cewa mutane da dama sun amfana, amma akwai bukatar kara wayar da kan mutane.
“Misali, a Zamfara, mutum fiye da 200,000 sun amfana daga wadannan shirye-shirye a cikin shekaru bakwai da suka gabata.
“An maimaita irin haka a fadin kasar kuma tuni ana zuba triliyoyin nairori a wadannan shirye-shirye masu amfani.

Kara karanta wannan

Tsaro: Dan majalisar PDP ya ce Buhari ya gaza, kawai a ba kowa dama ya mallaki bindiga a Najeriya

“Kai tsaye aka dunga turawa mutane kudi daga asusun bankuna ciki harda masu sukar gwamnati.
“Shugaban kasar ya yiwa kasar tanadi mai kyau, amma akwai bukatar a kara kaimi ta bangaren aiwatarwa da kuma tallata su.”

Kan ci gaban tattalin arziki, babban jigon na APC ya bayyana cewa Buhari ya tallafawa manoman Najeriya da dama ta shirin bayar da rance na ABP, yana mai cewa wannan ba boyayyen abu bane.

A cewar Idris, an baiwa manoma irrai da sauran kayan noma yana mai cewa shugaban kasar yayi namijin kokari, rahoton The Eagle.

“Wannan ne dalilin da yasa kasar bata wahala daga fatarar yunwa da ake ta tsammanin zai kasance saboda annobar korona da sauran abubuwan da ke addabar tattalin arziki.
“Buhari ya kuma yi kokari sosai a wajen yaki da rashawa kuma akwai kokarin da ake don magance matsalolin tsaro daban-daban da ke addabar kasar.”

Rikicin PDP: Ayu, Tambuwal da Sule Lamido Sun Gana Da Gwamnan Bauchi

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa tayi bayanin makomar Shugaban INEC da ake rade-radin tsigewa

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya isa jihar Bauchi a ranar Asabar domin ganawa da Gwamna Bala Mohammed.

Ayu ya samu rakiyar darakta janar na kungiyar kamfen din takarar shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, PM News ta rahoto.

Tawagar sun isa Bauchi da yamma sannan suka yi wata ganawar sirri tare da mai masaukinsu, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel