Buhari Ya Gaza, Ya Kamata Duk Dan Najeriya Ya Nemi Makami, Inji Dan Majalisar PDP

Buhari Ya Gaza, Ya Kamata Duk Dan Najeriya Ya Nemi Makami, Inji Dan Majalisar PDP

  • Dan majalisar wakilai ya fusata da yadda lamarin tsaro a Najeriya ke kara tabarbarewa a 'yan kwanakin nan
  • Ya bayyana bukatar a ba 'yan Najeriya daman su mallaki makamai domin iya kare kai daga barnar tsageru
  • Majalisa ta ba shugaban kasa Buhari wa'adin ya gaggauta shawo kan matsalar tsaro, abu ya gagara har yanzu

FCT, Abuja - Toby Okechukwu, mamban majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam'iyyar PDP ya bukaci gwamnatin kasar nan ta ba 'yan kasa damar mallakar makamai don kare kawunansu.

Ya bayyana hakan ne a duba da ya yi da karuwar ta'azzarar lamarin tsaro a Najeriya da kuma yadda gwamnati ta gaza kawo mafita.

Dan majalisar da ya taso daga jihar Enugu ya bayyana hakan ne a wata tattauna da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Dan majalisa ya ba da shawarin a ba 'yan Najeriya damar mallakar makamai
Buhari ya gaza, ya kamata duk dan Najeriya ya nemi makami, inji dan majalisar PDP | Hoto: Hon Toby Okechukwu
Asali: Facebook

Okechukwu ya yi tsokaci da cewa, lamarin rashin tsaro a Najeriya kara tabarbarewa yake, inda ya kara da cewa, shugabanci na gari ne kadai mafita ga duk wata manakisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Abin da zai kawar da wannan lamari kawai shine mu samu shugabanci na gari. Idan muka ci gaba a haka, ya kamata a bar 'yan Najeriya su kare kansu."

Duk da ba Buhari wa'adin kawo karshen matsalar tsaro, babu abin da ya sauya, inji Okechukwu

Ya kuma bayyana cewa, a baya majalisar dokokin kasa ta ba Buhari wa'adin ya tabbatar da kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, amma hakan bai kawo wani sauyi ba ko kadan a kasar nan.

Ya ce:

"Matsalar tsaro bata warware ba matukar ban yi tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ta hanyar da na saba ba. A jiha ta kwanakin baya an yi garkuwa da wani tsohon SSG da wasu dalibai da suke hanyar komawa jami’a, ta yaya zan ce tsaro ya inganta?”

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

A wani labarin na daban, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi batu mai ban dariya a fadarsa da ke Abuja yayin da yake martani ga zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na zaben 2023.

Shugaba Buhari, cikin barkwanci ya ba Tinubu da Shettima kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa, Leadership ta ruwaito.

Buhari wanda ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa jim kadan bayan shugabannin APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun kaddamar dashi, ya ce ya yi matukar farin ciki da zabo tsohon gwamnan na jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel